Na riga na shirya kutunguilar da zai naka Badaru da kasa a zaben 2019 – Sanata Ubale Shittu

0

Sanatan da ke wakiltar Jigawa ta Arewa Ubale Shittu ya lashi takobin ganin cewa gwamnan Jihar Mohammed Badaru bai koma kan karagar mulki a Jihar ba.

Shittu ya ce babu abin da zai hanashi tumbuke Badaru daga kujeran gwamnan Jihar.

” Da kuke ganina haka na gama shiri tsaf na shirya duk dabaru da kutunguilar da nake bukata don ganin na cimma buri na.

” Ina so in tsige shi ne don ba ya aikin komai a jihar, in banda mulkin kama karya da son kai babu abin da yake hi a Jihar.

” A shekarar 2015, ‘yan Najeriya sun fatattaki PDP dake kan mulki saboda babu abin da suka yi wa mutanen kasa.
Amma yanzu ba zan fadi muku irin shiri na ba amma tabbas sai naga bayan sa.

” Haba ace gwamna sai dai yayi ta raba kwangila ga matan sa da Iyalan sa. A 2019, za mu wayar wa mutane kai kan hadarin da ke tattare da sake zaben Badaru a matsayin gwamnan Jihar Jigawa.

Kakakin gwamnan Jihar, Bello Zaki, ya ce Shittu na fushi don gwamna Badaru yaki saka baki kan fushin da ‘yan mazabar sa suke yi da shi na mara wa Bukola Saraki baya da yayi.

Share.

game da Author