2019:TSAKANIN SOWORE DA SHITTU: ‘Kai karan kada miya ne, je ka nemi takarar kansila…, Inji minista Shittu

0

Minista Shitu: ‘Kai karan kada miya ne, je ka nemi takarar kansila, ba shugaban kasa ba.”

Sowore: ‘Tsoffin ‘yan alewa ba su iya ceto Najeriya, sai matasa sabbin-yanka-rake.”

Ranar Asabar ne wani gidan radiyon tashar FM da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo ya gayyaci Adebayo Shittu, Ministan Sadarwa na Gwamnatin Muhammadu Buhari, kuma a lokaci guda ya gayyaci mawallafin jaridar SaharaReporters, Omoleye Sowore, wanda a yanzu ya fito takarar shugaban kasa, inda suka yi tattanawa mai zafin gaske a tsakanin su.

Tattaunawar ta yi zafi, kuma ta ja hankali sosai, domin dimbin jama’a sun saurara kai-tsaye.

PREMIUM TIMES ta saurari shirin kai-tsaye daga gidan radiyon Fresh FM na Ibadan, kuma ga shi za ta gabatar wa masu karatun ta.

SOWORE: Minista na ji dadin haduwa da kai a nan gidan radiyo. Ina yi wa ministan gwamnati mai barin gadon mulki barka da zuwa. Na kira ka minista mai barin gado domin a 2019 za mu fatattaki gwamnatin Buhari.

SHITTU: Kai za ka fatattake mu, ko kuwa sai Allah ya kawo karshen mulkin mu? Wannan mafarki ne kawai ka ke yi. Gara ma ka farka, domin gari ya waye, safiya ta yi.

SOWORE: ‘Yan Najeriya za su fatattake ku yallabai. Kuma ba mafarki na ke yi ba. Gaskiya na ke fada maka, amma kai da ke mafarkin, idan ranar ta zo, ai za ka wartsake, ka gane mafarkin ka ke yi.

SHITTU: Shin wai kai Sowore, me ka ke takama da shi ne? Wane tasirin shiga zabe ka ke da shi a garin ku Ife ko kuma ko’ina a cikin fadin kasar nan?

SOWORE: Ai da tasiri na kuwa ka samu nasara a 2015 har aka nada ka minista. Domin ai kafin zaben, a cikin 2014 ‘yan Najeriya da dama ba su ma san ku ba, kai da sauran wadanda guguwar Buhariyya ta kawo kan mulki.

SHITTU: To ai kai dai ne ba ka san ni ba, saboda kai ba kowa ba ne, kuma ba komai ba ne, karan-kada-miya kawai ne kai.

SOWORE: Ai kuwa ni yaro da gari ne, abokin tafiyar manya, domin kai dai ba ka hau mulki ba, sai da jajircewar da na yi ni da sauran matasan kasar nan, mu ka ce a zabi APC. Mu ne mu ka duka, ka taka gadon bayan mu, ka hau mulki. Da ba mu duka kun hau gadon bayan mu ba, ko ka yi tsalle ba za ka iya hawan mulki a 2015 ba.

SHITTU:To wai kai me ka tsinana wa jama’a ne? Ba ka komai sai surutan banza da wofi kawai. Ni na fi karfin na zauna a nan da kai ka na surutai marasa kan-gado fa.

SOWORE: Haba Minista, daga mun zo mahawara sai ka fara bobbotai? Irin haka fa mutanen Jonathan su ka rika yi a 2014, a karshe su ka sha kasa. To ku ma hakan za mu yi muku a 20`19. Ci gaba da bobbobai ka gani. Najeriya ta masu kyakkyawan mafarki ce, iri na, ba ta tsoffin ‘yan alewa irin ku ba.

SHITTU (a fusace): Wai kai ka na jin shugabancin kasar nan na mutane irin ka ne? Ka je dai ka nemi kansila. Ni ma da dan majalisar jiha na fara, sannan na yi kwamishina sau biyu, kafin sannan kuma ni cikakken lauya ne ma. Amma duk kai ba ka san haka ba, saboda a lokacin ka na dan kucilin yaro kankane. Wai shekarun ka ma nawa tukunna?

Shugabancin kasa ba na yaran da ba su daina wasan kasa ba ne. Siyasar Najeriya ai ba irin siyasar yara ce da ka yi a jami’a ba. Ehe!

Ba dai ka ce ka fito takara ba? To da yardar Allah za mu kunyata ka, za ka kwashi buhun kunya ka koma inda ka fito.

BROWN(mai gabatarwa): To kai Sowore me ka ke takama da shi da har ka kudiri aniyar shugabancin Najeriya ka fito takarar zaben 2019?

SOWORE: Ka san dai ni ban fi shekaru 47 a duniya ba, amma na kusa shafe shekaru 30 a cikin siyasa, mun sha gwagwarmaya da gwamnati, ko gwagwarmayar kafa gwamnati. Na kafa jaridar da wannan gwamnatin ta rike a matsayin makamin yakin cin zaben 2015.

SHITTU: Shirme kenan. To ni kuma ina cikin siyasa tun lokacin da aka haife ka ma. Na kai shekara 40 ina siyasa. Kafin ma na shiga siyasa ni cikakken lauya ne. Don Allah bai kamata ka zo nan ka na yi mana shirme ba.

“In banda shirme ma ya kamar ka zai fito neman shugabancin kasar nan? Wa zai zabe ka? Sai dai shugaban kauyen ku Ife, amma ba dai Najeriya ba. Idan ka na mafarkin cewa shugabancin Najeriya garabasa ce, to ka fito din ka gani idan za ka iya kwasa.

Kai ne fa ka je ka buga karya da sharri a kai na, to ka yi hankali, sai na maka ka kotu domin ka gane kuren ka.

SOWORE: Ban buga karya a kan ka ba. Ma’aikatan ka ne suka rubuta takardar korafi a kan ka, su ka ce ka handami kudin sata, kuma ka na tauye musu hakki, ba ka biyan su albashi. Kafin in buga na kira ka, ka ki daukar waya ta.

Na yi maka tes, ba ka maida amsa ba, saboda kai a tunanin ka ni ba kowa ba ne, karan-kada-miya ne. To ai shikenan.
Amma ka san wani abu? Ka je ka kai ni kara kotu, idan na gurfana gaban alkali zan bude wani sabon littafin na ka(aka bushe da dariya).

Share.

game da Author