Hukumomin kasar Saudiyya a karon farko cikin shekara 35 sun amince a bude gidan sinima na farko a ranar 18 ga watan Afrilu a birnin Riyadh.
Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito wannan Labari, hakan zai share fagen bude wadansu gidajen sinima da zasu Kai kusan 100 a fadin kasar nan da shekarar 2030.
Malaman kasar Saudiyya ne suka fara yin raddi Kan gidajen kallo na sinima a shekaru kamar 40 da suka wuce wanda hakan yasa dole aka rufe su.
Ranar 18 ga wannan wata na Afrilu ne ake sa ran za a fara kallo a sinima ta farko a babban birnin kasar, Riyadh tun bayan rufe su.
Kamfanin gidajen sinima na duniya AMC, ne zai bude wadannan gidaje a manyan birane cikin shekara 5 masu zuwa.
Ana sa ran za a bude gidajen sinima kusan 40 a wadannan shekaru.