Fitaccen dan jaridar nan Ahmed Salkida da aka sani yana da alaka da Kungiyar Boko Haram ya bayyana cewa cikin ‘yan matan Chibok da Boko Haram suka yi garkuwa da su 15 ne kacal suka rage domin kuwa duk sauran sun mutu.
Salkida yayi dogon bayani kan halin da ‘yan matan suke a shafin sa na tiwita, inda ya ce cikin dalibai 113 da ake zaton har yanzu suna tare da Boko Haram 15 ne kacal ke da rai cikin.
” Kuma ma duk 15 din basu karkashin Shugaban Kungiyar, Abubakar Shekau domin suna tare da mazajen su ne da ya aurar wa.
” Idan kaga Shekau ya Iya wani abu a kansu toh sai dai Idan mazajen su sun mutu ko kuma an sake su nan ne ma fa zai ce wani abu.
” Sauran matan duk sun mutu a arangamar sojin Najeriya da ‘yan Boko Haram din.
Sannan kuma a gaskiya yadda gwamnati ta ke tsumulmular gaskiyar maganar ceto ‘yan matan Chibok da ma na Dapchi, abin sai a hankali don bai nuna cewa lallai suna son a kawo karshen Boko Haram a kasar nan.
” Kawai gwamnati ta daina yi wa mutane rufa-rufa domin babu sauran wasu dalibai da suka rage tare da Shekau, wani tattaunawa da ake cewa ana yi duk rudu ne. Labaran da ake yadawa ba gaskiya ba ne. ‘yan Najeriya su nemi a gaya musu gaskiya kawai.
Discussion about this post