KWALERA: Mutane uku sun rasu a Barno

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Barno Haruna Mshelia ya bayyana cewa mutane uku sun rasa rayukan su sanadiyyar kamuwa da cutar kwalera a jihar.

Ya fadi haka ne a lokacin da shugaban kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) Tedros Ghebrayesus ya ziyarci cibiyoyin kula da masu fama da irin wadannan cututtuka a Maiduguri.

Mshelia ya kara da cewa a cikin makonni biyu da suka wuce mutane 700 sun kamu da cutar kwalera a kauyukan Baga, Doron Baga da Kukawa.

Ya ce gwamnati da hadin guiwar WHO sun zage damtse don ganin sun dakile yaduwar cutar a wadannan kauyuka.

” A cikin makonni shida da suka wuce, gwamnatin Jihar tare da hadin guiwar WHO sun yi wa mutane allurar rigakafin cutar sannan mun kuma tsara shiri na wayar da kan mutane game da cututtukan Hepatitis B, zazzabin cizon sauro, shan inna, bakon dauro da sauran cututtuka.”

Mshelia ya kuma yi kira ga WHO da su ci gaba da mara musu baya wajen inganta kiwon lafiyar mutane a jihar.

A karshe Ghebrayesus ya tabbatar da ci gaba da mara wa jihar baya sannan yace za su gudanar da bincike a wadannan wurare da cutar Kwalerar ta bullo domin hana ci gaba da yaduwa wasu sassan jihar.

Share.

game da Author