Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba ta da masaniya game da korafin da dan jarida Ahmed Salkida ya yi cewa wai babu sauran ‘yan matan Chibok da suka rage tare da Boko Haram.
Idan ba a manta ba Salkida yayi dogon bayani kan halin da ‘yan matan suke a shafin sa na tiwita, inda ya ce cikin dalibai 113 da ake zaton har yanzu suna tare da Boko Haram 15 ne kacal ke da rai cikin.
” Kuma ma duk 15 din basu karkashin Shugaban Kungiyar, Abubakar Shekau domin suna tare da mazajen su ne da ya aurar wa.
” Idan kaga Shekau ya Iya wani abu a kansu toh sai dai Idan mazajen su sun mutu ko kuma an sake su nan ne ma fa zai ce wani abu.
” Sauran matan duk sun mutu a arangamar sojin Najeriya da ‘yan Boko Haram din.
Sannan kuma a gaskiya yadda gwamnati ta ke tsumulmular gaskiyar maganar ceto ‘yan matan Chibok da ma na Dapchi, abin sai a hankali don bai nuna cewa lallai suna son a kawo karshen Boko Haram a kasar nan.
” Kawai gwamnati ta daina yi wa mutane rufa-rufa domin babu sauran wasu dalibai da suka rage tare da Shekau, wani tattaunawa da ake cewa ana yi duk rudu ne. Labaran da ake yadawa ba gaskiya ba ne. ‘yan Najeriya su nemi a gaya musu gaskiya kawai.
Kakakin fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana cewa gwamnati ba ta da masaniya game da abubuwan da Salkida ya fadi.
” A sanin gwamnati dai dan jarida Salkida baya cikin jerin wadanda suke tattaunawa da Boko Haram tun a karon farko da aka sako ‘yan mata 100 sannan bashi cikin wadanda suke ci gaba da tattaunawa a halin yanzu domin sakin sauran ‘yan matan dake tare da Boko Haram din, saboda haka wannan wata magana ce da bam kuma sabuwa ga gwamnati.
” Idan ma akwai bayanai da gwamnati bata sani ba, har yanzu shi Salkida bai sanar da ita ba. saboda haka idan ana neman karin bayani, shine aya kamata a nema.