Jiya Asabar ne tsohon Ministan Tsaron Najeriya, Theophilus Danjuma ya zargi sojojin Najeriya cewa su na taimaka wa ana kashe mutane a jihar Taraba da sauran yankuna.
Ya ce sojojin Najeriya su na nuna son kai da bangaranci, inda suke hada baki su na barin mahara na kashe mutane a Taraba da sauran jhohin kasar nan.
Ya yi wannan furucin ne a wurin bikin yaye dalibai a Jami’ar Jihar Taraba, a Jalingo, babban birnin jihar.
Jawabin da ya yi wanda aka watsa a AIT, an yi ta tura furucin na sa a soshiyal midiya inda aka ruwaito ya na cewa jama’a su tashi su kare kan su da kan su.
Danjuma na nuni da cewa sojoji na taimaka wa makiyaya su na kashe mutane.
Wannan furuci na sa ya janyo masa fushin jama’a a fadin kasar nan, inda tuni da dama ke cewa ya zubar da girman sa, tunda har ya yi kiran da mutane su tashi su dauki makamai da kan su.
“Idan har ku ka zauna galala sai kun jira sojoji sun kare ku, to za a kashe ku daya-bayan-daya.
“Al’ummar Taraba da sauran yankunan Najeriya su tashi su kare kan su da kan su.” Inji Danjuma.
Furucin Danjuma zubar da girma ne -Sojojin Najeriya
Sai dai kuma nan da nan Hedikwatar Sojojin Najeriya ta maida masa kakkausan martanin cewa zargin da ya ke yi karya ne, ba gaskiya ba ne.
Sojojin sun nuna cewa ko kadan basu dauka mutum irin Danjuma zai maida kan sa kasa ya yi irin wannan kasassaba irin wadda sai gogarma ne kawai ke iya yin wannan danyar magana.
Musamman sun nuna rashin jin dadi, ganin cewa ya yi wannan kalami ne a lokacin da su ke kan ganiyar kokarin ganin sun dawo da zaman lafiya ya dore a kasar nan.
” Ya kamata jama’a su sani cewa sojoji ne a sahun gaba wajen sadaukar da rayukan su ana kashe su domin a tabbatar da samun zaman lafiya a Taraba.
“Misali, an kashe wani soja a Takum, wanda bayan an kashe shi, kuma aka datse masa kai, a ranar 16 Ga Maris, 2018.” Inji Texas Chuku.
Chuku ya kara da cewa ‘yan siyasa na sukar su don kawai sun ki yarda su yi musu abin da suke so a jihar Taraba, wato su yi bangaranci a batun fadan makiyaya da Fulani.
” A fili ta ke cewa tun daga lokacin da aka kafa sintirin ‘Exercise Ayem Akpatuma’ da ‘Cat Race’ a yankin Tivi, ita gwamnatin jihar Taraba ba ta bada hadin kai ga sojojin Najeriya ba. Saboda kawai sojoji sun tsaya ba su goyi bayan kowane bangare ba, kamar yadda ita gwamnatin ta so sojojin su mara mata baya a rikicin makiyaya da manoma.
Kakakin Hedikwatar John Agim, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa babu zancen gaskiya a cikin surutan TY Danjuma.
“Janar TY Danjuma, mutum ne da mu ke ganin girman sa, amma maganganun da ya furta duk kazafin ne, babu gaskiya a ciki.
Ya ce hukumar sojoji wuri ne mai da’a, shi ya sa ba su wasa, kuma idan aka tabbatar da zargi, to za su hukunta wanda ake zargin.
“Batun mu na mara wa wani bangare baya kuwa wannan ba gaskiya ba ne, kage ne, kazafi ne kawai.”
Danjuma ya yi wannan kakkausan zargi ne ganin irin kashe-kashen da ke faruwa sun yi yawa a kasar nan. Sai dai kuma mamakin da jama’a suka yi, shi ne bai taba yin irin wannan kakkausan magana a baya ba, musamman a lokacin da kabilar jihar sa, Taraba suka yi wa Fulani mummunan kisan gilla a Mambilla da kisan Adamawa da Numan da sauran wurare.
Yadda Danjuma ya yi wannan jawabi a Jalingo, jihar da aka yi wa Fulani kisan-gilla tare da sa musu takunkumin hana su kiwo da haddasa wa daruruwan su gudun hijira, hakan ma ya janyo masa kakkausan martani daga jama’a da dama.
Da ya ke bayani, ya ce tunda 2018 ta kama ake ta kashe-kashe a jihohi da dama, amma gwamnati ta kawar da kan ta, ta nuna kamar ta kasa shawo kan lamarin.
Ya ce irin yadda ake kashe-kashe ba ji ba gani, alamomi ne da ke ingiza mu a kan bin turbar kasar Somaliya, kasar da ta rifta cikin rikicin yake-yake tun 1991.
Danjuma ya yi babbar katobara — Ministan Tsaro
” Wannan kalami baa bin amincewa ba ne, kuma bai kamata kamar sa ya yi wannan kasassabar ba, domin wannan kira ne ya ke yi da kowa ya dauki makami a yi yakin kare-dangi kenan.” Inji Tukur Gusau, kakakin yada labaran Ministan Tsaro, Mansur Dan-Ali.
” Kowa na ganin irin kokarin da jami’an sojoji ke ta yi ba dare ba rana a kasar nan, wajen ganin sun tabbatar da zaman lafiya. Kuma ‘yan Najeriya na ci gaba da nuna gamsuwar su da yabawa kan irin wannan kokari da ake yi, fiye da yadda aka samu kasar a baya.”
“Don haka idan har wani na da korafi a kan wani abu na ba daidai ba da ya ke zargin sojoji sun yi masa, sai ya kawo hujjoji, inda nan take za a dauki kwakwaran mataki.”
Martanin Gwamnatin Jihar Taraba:
Kakakin gwamnatin jhar Taraba, Emmanuel Bello, ya ki yarda da bayanin da sojojin suka yi. Ya shaida wa PREMIUM TIMES ta hanyar sakon text cewa, “Ta ya aka yi mu ka ki gya musu baya? Ai ya kamata a fara yi mana cikakken bayanin wannan kakkausan zargin da aka yi mana, kafin mu maida martani tukunna.”
Ya ce gwamna Darius Ishaku ya rika aiki tare da jami’an tsaro domin ya tabbatar an dawo da zaman lafiya a jihar.
“Mu a koda yaushe a shirye mu ke da mu yi aiki tare a jami’an tsaro domin a tabbatar da zaman lafiya a jihar Taraba. Gwamna shi ne babban jami’in tsaron jihar sa, don haka a shirye ya ke ya hada kai da kowane bangarenn jami’an tsaro a samu zaman lafiya.”
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga cikakken labarin yadda Gwamnatin Jihar Taraba ta rubuta wa Kwamishinan ‘Yan sandan jihar wasikar ya saki dukkan wadanda aka kama da laifin yi wa Fulani kisan kiyashi a Mambilla. Labarin ya fito fili ne bayan an sake su gaba dayan su.