Sanata Dino Melaye ya karyata rahoton da Sahara Reporters ta buga a jiya Asabar cewa ya tsere kasar waje.
Melaye ya karyata wannan zargin ne a cikin wata wasika da ya rubuto wa PREMIUM TIMES, inda a ciki ya bayyana cewa ya fi karfin ya gudu ya bar iyalin sa a Najeriya don kawai ya na fama da rigingimu daga wasu masu bin sa da mugun nufi.
Sahara Reporters ta buga labarin cewa Dino Melaye ya arce, saboda ya fahimci za a tsige shi daga sanata a ranar 29 Ga Afrilu, 2018, idan INEC ta shirya masa kiranye.
A cikin rahoton na Sahara Reporters, ta ce majiya ta shaida mata cewa Melaye ya ce ba zai dawo Najeriya ba, har sai an canja wata gwamnati.
Ta kara da cewa Gwamna Yahaya Bello ne ke son ganin bayan sa. Sannan kuma Melaye ya nuna haushi da fushin sa kan Shugaban Majlisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, ganin yadda bai nuna damuwa da kokarin ya fitar da Melaye din daga cikin tsomomuwar da ya afka ba.
Melaye dai ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa a yanzu haka ya na kasar waje, amma bai ce ga kasar da ya ke ba, kuma bai bayyana ainihin abin da ya kai shi ba, bai kuma aza ranar dawowa ba.
Ranar 25 Ga Afrilu ne INEC ta shirya yi masa sabon kiranye, tun bayan da Kotun Daukaka Kara ta bai wa hukumar zaben iznin ci gaba da kiranyen a farkon makon nan.
Za a kammala tantance kiranyen a ranar 29 Ga Afrilu.