An tsinto Shugaban APC bangaren Hunkuyi, Danladi Wada a Zariya

0

Bayan sanar da bacewar Shugaban jam’iyyar APC bangaren Sanata Suleiman Hunkuyi, Danladi Wada da Iyalan sa suka yi a ranar Asabar daga fita Sallar Asuba, kwatsam sai gashi an sami sanarwan tsintuwar sa a wani masallaci dake Unguwar Dan Magaji dake Zariya.

Kakakin jam’iyyar APC na bangaren Hunkuyi, Murtala Abubakar ne ya sanar da haka sannan ya kara da cewa tabbas masu garkuwan da suka gudu da Danladi sun bukaci ya saka hannu a wata takarda cewa ya sauka da ga kujerar shugabancin jam’iyyar na bangaren Hunkuyi, sannan sun sa shi ya fadi haka a na’urar daukar magana.

” Wani Dan siyasa ne da ya san Danladi Wada ya gane shi a wannan masallaci a Zariya, bayan Sallar Asuba, sannan ya kamo masa hannu ya fito da shi gari.”

Idan ba a manta ba a jiya ne Iyalan Danladi Wada suka sanar da sace mahaifin su daga fita Sallar Asuba a Unguwar Rimi dake garin Kaduna.

Kamar yadda babban dan Wada Abdulmumini Wada ya shaida wa PREMIUM TIMES ya ce mahaifin su ya fita sallar Asuba ne da wajen karfe biyar da rabi amma har yanzu bai dawo gida ba sannan basu san inda yake ba.

” Gashi babu yadda za a iya neman sa ta waya domin duk wayoyin sa na gida. Yanzu dai muna zaton masu garkuwa ne suka arce da shi.

Bayanai sun nuna cewa hatta jami’an tsaro da aka tuntuba ko yana tare da su ne, sun ce basu da masaniyar inda Danladi ya ke zuwa yanzu.

Share.

game da Author