Iyayen daliban sakandaren Dapchi, sun bayyana irin hudubar da Boko Haram su ka taraq su, suka yi musu bayan sun maida musu ‘ya’yan su jiya Laraba da safe.
Iyayen sun ce bayan da suka ajiye yaran, Boko Haram ba su bar garin da gaggawa ba, sai da suka tara jama’a suka yi musu wa’azi da huduba.
‘‘Mun cika da murna a cikin garin Dapchi a lokacin da muka fara ganin motoci dauke da yaran mu sun shigo cikin gari da misalin karfe 8 na fase.” Inji Ibrahim Hussaini, wani mazaunin Dapchi.
“Sun maido yaran daga nan sai suka ce mana kada mu bar wadannan yara su koma karatun boko, kuma su abin da suke yi, ba ta’addanci ba ne, jihadin yada addinin Musulunci ne.” Inji Hussaini, wanda shi ma kanwar sa na cikin wadanda aka sace, kuma aka dawo da ita.
Shi kuwa Bukar wanda shi ne sakataren kungiyar iyayen yaran da aka sace ‘ya’yan su, ya bayyana cewa tun cikin dare aka kira su daga garin Gumsa, aka ce musu ga Boko Haram nan sun ajiye yaran garin biyu da aka sace, amma sun tunkaro Dapchi za su maido sauran yaran.
Ya ce lokacin da ya bayyana wa jama’a wannan labarin, sai jama’a suka fara razana, aka rika gudu ana boyewa.
Kacalla ya ce amma sai shi da iyayen yaran da aka sace suka fito suka tsaya cirko-cirko na kallon yadda Boko Haram suka kutsa cikin garin Dapchi dauke da yaran a cikin motocin da suka yi amfani da su suka sace su, kwanaki 30 da suka gabata.
Ya ce nan da nan ya rutuma a guje, ya je ya tarbi yaran, har ma ya karbi wayar daya daga cikin ’yan Boko Haram ya rika daukar hotuna tare da yaran.
“Amma mu iyayen yaran da aka sace din, ba mu gudu mun boye ba, domin ba za mu iya gudu mu bar ‘ya’yan mu ba.
” Bayan sun shigo, suka ce mana sun maido mana yaran ba wai don wani ya biya su ko sisi ba, amma don karin kan su don ganin damar su ne kawai suka maido su. Daga nan muka yi ta yi musu godiya. Daga nan suka ce kada mu sake mu maida yaran makarantar boko. Muka ce musu to ba za mu maida su din ba. Suka ci gaba da yi mana huduba da wa’azi. Muka ce mun ji, mun kuma dauka.
“ Sun rika miko mana hannu, mu na gaisawa, su na ce mana mu yafe musu duk irin kuncin da suka jefa mu. Daga nan kuma suka ce mu zo mu dauki hotuna. Suka rika fito da wayoyin su, muka gwamutse mu da su, su na daukar mu hotuna.”
Majiya daga Dapchi ta ce Boko Haram sun bar garin da misalin karfe 9 na safe. Amma ba su yi nisa ba, tayar wata motar su daya ta yi faci, har suka tsaya suka canja wata.
Yaran ba su dade sosai ba daga nan sai aka zo aka kwashe su aka tafi da su asibitin Damaturu, daga nan kuma aka wuce da su Abuja.
Majiya a cikin jami’an sojoji a Yobe ta ce wa PREMIUM TIMES za a saki yaran ranar Laraba da safe.
Wani jami’in soja a Dapchi, ya shaida wa manema labarai amma ya ce a boye sunan sa, an ce kowanen su ya kwana da shiri, Boko Haram za su maido yaran da kan su, kuma dukkan su su janye daga inda aka girke su.
“Daga nan sai sojoji suka janye, suka yi kwanton bauna a bayan gari, su na jiran ko da Boko Haram za su canja tunani su bude wuta su na kai wa jama’a farmaki.
An ce su ma sojojin da ke wajen gari daidai mashigar garin, wadanda suka hana ‘yan jarida da matafiya shiga garin Dapchi, sun yi sauri sun janye jiki a lokacin da su ka hango kwanba din motocin Boko Haram sun darkako garin Dapchi.