Sanadiyyar sace ‘yan matan makaratar sakandaren kwana dake garin Dapchi, jihar Yobe da Boko Haram suka yi, gwamnatin jihar Barno ta bada umurnin rufe duk makarantun sakandare na kwana dake wajen garin Maduguri.
Kwamishinan aiyukan cikin gida, yada labarai da al’adun gargajiya na jihar Muhammed Bulama ne ya sanar da haka ranar Laraba inda ya kara da cewa gwamnati ta dauki wannan matakin tare da wasu matakan inganta zamantakewar mutanen jihar tun a wani zama da kwamitin tsaro da ya hada da jami’an tsaro, sarakunan gargajiyya da wakilan gwamnatin suka fara yi ranar 15 watan Maris.
Sauran matakan inganta rayuwar mutane da gwamnati ta dauka sun hada da:
1. Samar da tsaro a kananan hukumomin Bama, Gwoza da Dikwa kafin a fara dawowa da ‘yan gudun hijira dake zama a garuruwan.
2. Bude hanyar Maiduguri – Bama – Banki wanda ta yi shekaru uku a rufe.
3. Hukunta duk wanda aka kama yana taimaka wa Boko Haram baya.
4. Bude wuraren rajista da na’ura wa maniyata aikin hajjin bana, da dai sauran su.