2019: INEC na kokarin yi wa mutane miliyan 80 rajista

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, bayyana cewa ta na kokarin tabbatar da cewa ta samu har mutane milyan 80 da za su kada kuri’a a zabukan 2019.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, a lokacin da yake ganawa da kungiyoyin sa-kai da suka ziyarce shi.

Yakubu, wanda Kwaishinan Zabe na Kasa, Okey Ibeanu ya wakilta, ya ce ya zuwa yanzu dai akwai akalla kusan mutane milyan 73 masu rajista a Najeriya.

Ya ce a irin yadda aikin rajistar ke tafiya, alamomi na yin nuni da cewa za a iya samun masu rajista har milyan 80 din ya zuwa lokacin da za a rufe yin rajista.

Ya ce INEC ta kashe akalla naira biliyan 115 zuwa biliyan 120 a zaben 2015 kacal.

“Zabuka sunn tunkaro, kuma kun san zabe ba abu ba ne mai arha, ya na ci wa kasar nan kudade masu yawan gaske. Domin an kashe kusan naira bilyan 115 zuwa bilyan 120 a zaben 2015.

“Idan aka yi la’alari da zaben 2015 da na 2019 mai zuwa, to za a ga cewa canjin kudin kasashen waje zai shafi zaben 2019.

“Zak u iya lissafawa ku gani. An canja dala a kan naira 150 farashin gwamnati a zaben 2015. Yanzu kuma dala ta na naira 300 farashin gwamnati.”

“Yakubu yace INEC ta yi iyar kokarin ta wajen ganin ta takure kasafin zaben 2019 yadda zai yi daidai da halin da tattalin arzikin kasar nan ya ke ciki.

Daga nan sai ya nemi hadin ka da kungiyoyin sa-kai domin a shawo kan kashe makudan kudade wajen gudanar da zabe a kasar nan.

Ya ce tuni INEC ta mika wa gwamnatin tarayya kasafin kudin da za ta kashe a zaben 2019, yanzu kawai ba’asi ta ke jira daga gwamnati.

Share.

game da Author