Tsohon mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkar siyasa, Ahmed Gulak ya watsar da jam’iyyar PDP yau, inda ya tattara komatsan sa da dubban ‘yan jam’iyyar zuwa APC.
Gulak ya bayyana cewa ya yi haka ne tare da dubban magoya baya, 42,000 daga kananan hukumomi 21 na Jihar cewa jam’iyyar ta rube ta zama kaya.
Gulak ya ce yanzu dai sun yi jana’izar PDP a Jihar Adamawa.
Ya ba da misalin yadda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya canza jam’iyya har sau biyar cewa kowa na da ‘yancin canza jam’iyya kamar yadda doka ta yardar wa duk dan kasa.
” Atiku daga PDP, ya koma ACN, sannan ya dawo PDP daga nan ya koma APC gashi yanzu ya koma PDP.”