Rashin motsa jiki, taba, giya na haddasa karin tabarbarewar lafiya a jikin mutum – WHO

0

Kungiyar Kiwon Lafiyan ta duniya WHO ta koka kan yadda mutane suka yi watsi da kula da Lafiyar su ke haddasa yawan kamuwa da cutukan da za a Iya guje wa kamuwa da su.

WHO ta ce irin wadannan cutuka sun Karu a duniya ne saboda yawan shaye-shayen taba sigari, giya, rashin cin abincin da ya kamata da rashin motsa jiki.

WHO ta ce bisa ga binciken da ‘International Diabetes Foundation’ ta gudanar ya nuna cewa Mutane miliyan 415 na dauke da cutar siga sannan mutane miliyan 14 daga cikin su daga kasashen Afrika suke.

WHO ta kuma kara da cewa binciken ya nuna cewa adadin yawan mutanen dake dauke da cutar siga zai iya ninka wa nan da 2040 idan ba a tashi tsaye ba.

Sakamakon haka ne kungiyar WHO ta kafa wata kwamiti na musamman domain nemo hanyoyin da za abi a kawar da wadannan cutuka.

Mambobin Kwamitin sun hada da shugaban kasar Uruguay Tabaré Vázquez, shugaban kasar Sri Lanka Maithripala Sirisena, shugaban kasar Finland Sauli Niinistö, ministan kiwon lafiya na kasar Russia Veronika Skvortsova da tsohon ministan kasar Pakistan Sania Nishtar.

Share.

game da Author