Dalilan da ya sa Buhari ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya -Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya su kwantar da hankalin su tunda amanar kasar nan ta na hannun Shugaba Muhammdu Buhari.

Lai ya fadi haka ne a wani dan kwarya-kwaryan taro da ya yi tare da ma’aikatan Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Madrid, babban birnin kasar Spain ranar Asabar.
.
Ministan ya ce ba kamar irin labaran karairayin da ake watsawa a soshiyal midiya ba, to Najeriya ta samu ci gaba sosai a fannin tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Ya ce dama kuma su ne manyan harsasan da aka kafa ginshikin wannan gwamnatin a kan su.

“Ku daina amincewa da duk karairayin da ku ke karantawa a soshiyar midiya. Najeriya ba cikin halin yaki ko cikin rikice-rikice ta ke ba.” Haka jami’in yada labaran sa, Segun Adeyemi ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa wadanda ba su fatan kasar nan da gwamnati da alheri, a kullum su na kashe miliyoyin nairori domin su damalmala gaskiyar irin halin ci gaban da ake samu a Najeriya, domin kawai a rika kallon wannan gwamnatin a matsayin wadda ba ta iya shugabanci ba.

Ya ce gwamnati ta taka rawar gani a fannonin ayyukan noma, ciyar da daliban makarantu, samar da ayyukan yi da sauran su.

Share.

game da Author