Bangaren APC ta dakatar da Uba Sani, Abdu Kwari, ta yi wa El-Rufai wasikar gargadi

0

Bangaren APC ta dakatar da Uba Sani, Abdu Kwari, ta yi wa El-Rufai wasikar Gargadi

Rikicin Jam’iyyar APC a Kaduna sai kara tabarbarewa yake yi tun bayan raba jiha da akayi tsakanin Sanata Suleiman Hunkuyi da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Idan ba a manta ba, Hunkuyi ya fadi a wani taro da ya halarta cewa daga yanzu fa yaja daga da gwamnan jihar Kaduna, cewa ko ana-ha-maza ha –mata sai sun tsige gwamna El-Rufai daga kujerar gwamnan jihar Kaduna a 2019. Bayan haka kuma ya kaddamar da sabuwar bangaren jam’iyyar APC mai suna ‘APC Aspirant Forum’.

Hunkuyi ya ce babu abin da zai hana su yin duk abin da za suyi su ga cewa El-Rufai bai koma gidan gwamnatin Kaduna ba a 2019.

Bangaren jam’iyyar APC a Kaduna yau ta rubuta wa El-Rufai wasikar gargadi, cewa yana yi wa jam’iyyar zagon kasa, da yayi wa jam’iyyar bayani cikin awowi 48 ko kuma jam’iyyar a jiha ta dau matakin gaggawa kan sa.

Sannan ta dakatar da mai ba gwamna El-Rufai shawara kan harkar siyasa, Uba Sani, da kwamishin kudin jihar.

Jim kadan bayan sun aika wa fadar gwamnanti wannan wasikar gargadi, sai El-Rufai ya mai da wa wannan bangare na APC shimfidaddiyar amsa.

A wasikar sa El-Rufai ya ce ya ji duk gadarar da Sanata Hunkuyi yayi cewa wai sai ya cire El-Rufai daga kujerar gwamnatin jihar Kaduna ya dora kan sa.

“ Abin da nake so Hunkuyi ya sani shine kada ya manta yadda yayi ta yi wa wadanda yake tare dasu yankan baya don ya zama gwamnan jihar Kaduna, amma hakan bai yiwu ba. Ya je ya kafa bangaren jam’iyyar APC a gidan sa wai ita ce jam’iyya. Ya sani cewa abin da yake so ba zai samu ba domin mutanen jihar Kaduna kai har da na garin sa Hunkuyi sun shaida abin da muke yi wa talakawa.

“ Ruwa ne ya kare wa dan kada, Hunkuyi na neman inda zai rabe ne kawai. Amma wannan jam’iyya za ta san yadda za tayi duk makarkashiyar da suke shirya mata.

Da ya dan yi tsokaci game da kokarin gyara makarantu da gwamnatin jihar tayi, El-Rufai yace gwamnatin san a yin haka ne don talakawa, kuma babu abin da zai sa gwamnati ta karkata akalar ta zuwa wani wurin.

Darektan yada labaran jam’iyyar APC, na jihar Kaduna, Tanko Wusono, ya gargadi wannan bangare na APC, da su shiga taitayin su sannan su guji yin abin da zai kawo rabuwar kai a jam’iyyar.

Sannan kuma ya ce za su duba korafe-korafen da wannan bangare na APC ta kuma za ta dau matakin gaske game da irin wadannan zantuka da ta zuro, a wasikar da suka yi wa gwamnan jihar kuma zata hukun ta duk wanda ya saba dokar jam’iyyar ko shi waye.

Share.

game da Author