Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta sanar cewa wata babbar mota ta nike mutane hudu tare da motoci biyar a karamar hukumar Jos ta kudu jihar Filato.
Kakakin rundunar Terna Tyopev ya sanar da haka a yau Alhamis wa PREMIUM TIMES ta wayar hannu inda ya kara da cewa hadarin ya faru ne a shataletalen Mararaban Jama’ar ranar Laraba.
Burkin Motar ta ki mamawa a daidai motar ta shawo wannan shataletale, sanadiyyar haka ya hau wadannan mutane, sannan ya bubbuge motoci har biyar.
” Mun kama shi direban motan mai suna Abdulaziz Abdulraman dan shekara 25 sannan mutane hudu da suka rasu mun kai gawan su dakin ajiye gawa dake asibitin Ola karamar hukumar Jos ta kudu’’.
Discussion about this post