A yau Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnati za ta hukunta duk wadanda suka kai ko ke da hannu a harin da aka kai wa manoma a kananan hukumonin Guma da Logo dake jihar Benue.
Ministan aiyukkan cikin gida Abdulrahman Dambazau ne ya sanar da haka a ziyarar da ya kai jihar bayan tattaunawa da yayi da gwamnan jihar.
Ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi kasa kasa ba wajen hukunta wadanda suka aikata wannan mummunar aiki a jihar ba.
Daga karshe gwamnan jihar Samuel Ortom ya tabbatar wa mutanen jihar cewa gwamnati na nan kan bakan ta na hana kiwo a jihar ba.