Wasu mata a yau Alhamis, a garin Ado Ekiti, sun bayyana yadda aka sayar da ’ya’yan su mata ga dillalan cinikin bayi a Libya.
Matan sun bayyana cewa an rudi ’ya’yan na su ne da niyyar cewa za a sama musu aikin yi mai albashi da yawa a Dubai.
Sun bayyana matsanancin kuncin da su da ’ya’yan nasu su ka shiga ne bayan da jami’an ’yan sanda su ka cafke wata mata mai suna Dada Ogundare, da ake zargi da laifin yin safarar ’yan matan zuwa wani sansanin tattara bayi a Libya.
’Yan sanda a Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, sun gabatar da Ogundare ce tare da wani fasto mai suna Omoseeke Komolafe.
An ruwaito cewa su biyun sun karbi wasu makudan kudade daga hannun iyayen yaran domin shirya tafiya da su Dubai.
Sai dai kuma su wadanda ake zargin, sun bayyana cewa taimako ne su ka yi wa yaran da nufin fita da su su sama musu aiki kasashen waje, amma ba su san za su karke a matsayin bayi a cikin kangin bauta ba.
Wadanda aka bautar din sun bar Najeriya ranar 25 Ga Nuwamba, su ka nausa cikin sararin sahara, maimakon su hau jirgin sama kamar yadda ka yi musu alkawari. Maimakon a nufi da su Dubai kamar yadda aka yi musu alkawari, sai aka nausa da su cikin Libya.
Daya daga cikin iyayen matan, mai suna Magareth Olurunfemi, ta bayyana cewa sai daga baya mummunan labari ya zo musu cewa ‘ya’yan su na can an sayar da su a Libya su na bauta a matsayin bayi.
Kamar yadda ta bayyana, an yi ta kokarin a dawo da yaran gida, amma sai wadanda ke rike da yaran su ka ce sai an biya diyyar naira milyan 1.2 a kan kowace yarinya daya.
Ta ce ita da wannan fasto da ake zargi, duk mambobin jam’iyyar PDP ne, kuma duk mazabar su daya da Mataimakin Gwamnan Ekiti, wato mazabar Ikere Ekiti.
Olurunfemi ta ce, Komolafe ce ta shaida mata cewa wai Mataimakin Gwamna ya bada guraben aiki hudu ga ’ya’yan matan jam’iyya, za a tafi da su Dubai a ba su aiki, amma sai an bayar da naira 150,000 domin a yi cuku-cukun tafiya.
Ta ce ta fara shiga damuwa ne tun da ta ga an dauki tsawon lokaci ba ta sake jin duriyar ‘yar ta ba.
“Sai a ranar 10 Ga Disamba ne na samu na yi magana da yarinyar tawa, inda ta ce min su na wani sansanin cinikin bayi a Libya, inda aka sayar da su a matsayin bayi.”
Ba Olurunfemi ce kadai ta yi magana ba, ita ma Feyisayo Adebayo, wadda ita a halin yanzu ma ta na da tsohon ciki ne, tare da ’yar ta aka hada aka sayar.
Sai dai wadanda ake zargin din su nce ba su karbi wasu miliyoyin kudi a hannun iyayen yaran ba.
Discussion about this post