An kai wa gwamnan Edo hari; “Muna neman shugaban BUA ruwa a jallo” – Rundunar ‘Yan sanda

0

A wata takarda da ya fito da yammacin Alhamis din yau daga fadar gwamnatin jihar Edo, ya sanar cewa an kai wa tawagar motocin gwamnan jihar Edo hari.

Wanda ake zargi da shirya wannan hari kamar yadda gwamnatin jihar ta sanar shine Yusuf Binji, shugaban kamfanin Bua.

Idan ba a manta ba ana zaman doya da manja ne tsakanin kamfanin Dangote da na Bua kan asalin mai mallakin wani sansanin da ake hako sinadarin yin siminti a jihar.

A sanarwan da Robin Crusoe, kakakin gwamnan ya sa wa hannu, ya ce tuni ‘yan sanda sun fantsama neman shugaban kamfanin Bua Yusuf Binji cewa wai shine ya shirya wannan hari da aka kai wa tawagar gwamnan.

Share.

game da Author