NDE ta horas da matasa 2,150 sana’o’in hannu a Kebbi

0

Jami’in hukumar samar da aikin yi na kasa NDE rashen jihar Kebbi Mohammad Zogirma ya bayyana cewa hukumar ta horas da matasa 2,150 sana’o’in hannu a jihar.

Zogirma wanda ya sanar da haka wa manema labarai a Birnin Kebbi ya ce sun zabo matasan ne daga kananan hukumomi 21 dake jihar sannan sun horas da su ne na tsawon shekara daya (tsakanin watanni Janairu zuwa Disambar 2017) .

Ya ce matasan sun koyi sana’o’in hannun da suka hada da sana’ar Tela, kwaliya, kafinta, dukanci, dinka jaka, aski, sarrafa kanfita da sauransu.

Daga karshe ya yi kira ga matasan da su yi amfani da wannan dama da suka samu wajen inganta rayuwar su.

Share.

game da Author