Hukumar gudanar da bincike a California dake Amurka ‘Kaiser Permanente research’ ta yi kira ga iyaye mata da su shayar da ‘ya’yan su har na tsawon akalla watanni 6 nonon uwa.
Hukumar ta ce yin haka na kare iyaye mata daga kamuwa da cutar siga wato ‘Diabetes II’.
Wacce ta jagoranci nazari da bincike kan haka Erica Gunderson ta bada misalin cewa idan mace ta shayar da dan ta nono na tsawon watanni 6 tana samun isasshen kariya daga kamuwa da cutar siga.