Yadda za ka mallaki rajistar zabe a saukake

0
Hukumar zabe mai zaman kanta ka kasa, INEC, ta saukaka wa ‘yan Najeriya yadda za su mallaki rajistar jefa kuri’a zaben 2019, tare kuma da fito da hanyar da za a binciki idan rajistar da mutum ya yi ta na nan daram.
Idan ba a manta ba, INEC ta fara aikin cigaba da yin rajistar zaben 2019, tun a ranar 27 Ga Afrilu, 2017, domin duk wani wanda ya cancanta ya yi zabe ya samu ya mallaki rajistar sa ta Katin Dindindin na PVC.
A kan haka ne kuma yanzu INEC ta fito da wasu hanyoyi biyu na mallakar Katin Dindindin na PVC.
Mataki na farko shi ne dan Najeriyar da ya cancanta, amma kuma a baya bai yi rajista ba, sai ya fito yanzu a Shirin Yin Rajista na 2 da ke gudana a wasu jihohi, har da Abuja, ya je ya yi rajista.
INEC ta ce ana fara aikin yin rajistar ne daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana, daga ranakun kowace Litinin zuwa kowace Asabar.
Za a kuma iya shafin yin rajista a online, ta soshiyal midiya mai suna: http://www.inecnigeria.org/?inecnews=registration-area-centres-continuous-voter-registrationcvr-phase-2
 
Za a iya shiga wannan hanya ta yin rajista a intanet a jihohi 12 da suka hada da: Anambra, Sokoto, Oyo, Kwara, Jigawa. FCT, Ebonyi, Delta, Cross River da kuma Bauchi.
Sai an shiga cikin shafin a intanet, za a ga bayanan yadda za a yi rajistar. Sannan kuma kowace jiha ta ware sunayen kananan hukumomin da za a yi rajista da kuma sunayen santa-santar da za a yi rajista a kowace karamar hukuma.
 
Akwai kuma mataki na yin rajista na biyu, wanda shi kuma wanda ya rigaya ya y i rajista a baya, to a nan ne zai bincika ya tantance ko an yi masa rajistar ko a’a. Shi kuma zai shiga:   http://voterreg.inecnigeria.org
Wanda ya shiga wannan zauren rajistar zaben za a nuna masa inda zai shiga ya cike wani fam, inda za a tambaye shi jihar da ya ke zaune, sunan mahaifin sa da kuma VIN lambar sa.
A inda aka samu akasi mutum ya manta VIN lamba din sa, to akwai inda zai cike rana, wata da shekarar da yay i rajista domin a tantance.
Sakataren Shugaban Hukumar Zabe, Rotimi Oyekanmi, ya bayyana cewa duka a cikin jihohi 12 ne ake gudanar da rajista ta hanyar online, a daya gefen kuma ana ci gaba da aikin rajista ta game-gari a sauran jihohi 36 na kasar nan.
INEC ta kara bayyana cewa cibiyoyin tuntuba na Citizens Contact Centre na nan, za a iya tuntubar su ta: 070 2255 4632.
Share.

game da Author