Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa daga yau kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biafra IPOB sun zama kungiyar yan ta’adda a kasa Najeriya.
Rundunar Sojin ta sanar da haka ne yau a wata sanarwa da ta fitar yau.
Tace bayan ta kammala duba dukkan bayanai akan ayyukan kungiyar ta gamsu cewa kungiyar ‘yan Ta’adda ne a kasar nan.
Cikin dalilan da Rundunar Sojin ta bayar da sune suka zama hujjojinta na yin haka hada da:
1 – Kungiyar ta kafa wata rundunar mayaka na sirri
2 – Ta kafa jami’an tsaro na Biafra mai suna ‘Biafra National Guide’
3 – Suna yi wa mutane kwace a hanyoyi
4 – Kai farmaki da makamai ga jami’an yan’sanda da Sojoji
5 – Sun kai wa Sojoji hari cikin jagorancin shugabansu Nnamdi Kanu da kokarin kwace makamin wani soja.
6 – Neman kwace bindigar wata jami’ar soja.
” Rundunar Soji ta na kira ga iyaye da su gargadi ya’yansu su nisanci shiga kungiyar IPOB din domin duk wanda aka samu aciki ya zama dan ta’adda.”