Jam’iyyar APC ba ta tilasta wa Aisha Alhassan ta ajiye aikin ta ba – Bolaji Abdullahi

0

Jam’iyyar APC ta titsiye Ministar Harkokin Mata, Aisha Alhassan, inda ta shafe tsawon sa’o’i biyu ta na amsa tambayoyin da aka rika sharara mata.

Zaman, wanda aka yi ranar Alhamis a hedikwatar jiam’iyyar, a Abuja, an fara shi ne tun misalin karfe biyu na rana, aka kammala karfe hudu na yamma.

Shugaban jam’yyar APC, Odige Oyegun da kan sa ya jagoranci zaman tattaunawar jin ba’asin Mama Taraba.

Ministar dai ta fito a fili ta ce a siyasa Atiku Abubakar ne ubangidan ta, kuma inda Buhari zai sake tsayawa kuma Atiku shi ma ya fito takarar shugaban kasa a 2019, to Atiku za ta bi.

Ya sake yayar da rudun siyasa kwanaki biyu da yin wancan furuci, inda ta ce ita ba ta iya munaficci ba, don haka gaskiyar ce ya fada, idan ma za a cire ta daga mukamin minista, to ba za ta damu ba.

Fitowar ta ke da wuya sai mnema labarai su ka tare ministar domin ta ba su labarin abin da suka tattauna. Alhassan ta ce ai idan ta magana, to ta yi shisshigi, domin jami’in yada labarai na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ke da alhakin yi wa jama’a bayani.

Bolaji ya shaida wa ‘yan jarida cewa sun gayyaci ministar ne domin su ji abin da ta fada da kan ya. Ya ce ta na da ‘yancin yin magana, amma lokacin yin maganar ne bai dace ta yi ba.

“Kin ga dai zaben nan sai 2019, kuma 2018 ma ba ta zo ba tukunna. Ashe kenan ta yi saurin fito da maita a fili.

” Amma ba wani abin tashin hankali ba ne, don ta nuna wani dan takara ta ke so. Kawai abin dubawa shi kan sa Atiku bai fito kuru-kuru ya ce zai tsaya takara a 2019.”

Bayan haka ya kara da cewa jam’iyyar bata umurci minista Aisha ta ajiye aikinta na minista ba, sai dai jam’iyyar ta nuna rashin jin adinta kan irin maganganun da tayi da ta ziyarci Atiku.

” A matsayin ta na minista a wannan gwamnati ba za mu ji dadi ba a ce ta furuta irin wannan kalamai.”

Share.

game da Author