Rasuwar dan autan mawaka, Lil Ameer ta girgiza Jama’a

5

Jiya cikin dare aka bada sanarwar rasuwar shagararren yaro kuma mawakin Hausa na Hip Hop da aka sani da Lil Ameer, a Kano.

Ameer ya rasu ne Alhamis da dare sanadiyyar hatsarin da ya ritsa da shi, a cikin Keke NAPEP, wato A Daidata Sahu.

A ta bakin Shugaban Jami’ar NOUN, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya ce su Ameer sun yi hatsari ne a cikin Keke NAPEP, inda tsautsayi ya faru, bayan ya fado kasa, sai wata mota ta take shi.

Dan autan mawakan dai ya na da farin jini ga yara, matasa har ma da manya manazarta wakokin Hausa.

Kwana daya kafin rasuwar sa, sai da Ameer ya je gidan talbijin na Farin Wata.

Takaitaccen Tarihin Lil Ameer

An haifi Ameer a 2003, cikin birnin Kano. Ya fara waka tun ya na shekara 9 a duniya, kuma ya na waka ne da goyon bayan iyayen sa, hasali ma mahaifiyar sa ce ke rubuta masa wakokin.

Ameer ya fitar da album da dama, kuma a gidajen radiyon FM na Kano, tauraruwar sa na haskawa, domin wakokin sa na daga cikin mashahuran wakoki goma da ke haskawa a gidajen radiyon Ray Power, Dala FM da sauran su.

Share.

game da Author