Maganganun da Dickson yayi akan Kwamitin Makarfi ra’ayinsa ne ba na jam’iyyar ba – Inji Adeyeye

0

Kakakin jami’yyan PDP na bagaren Ahmed Makarfi Dayo Adeyeye ya ce maganganun da gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya yi akan cewa wai jam’iyyar na bangaren Makarfi ta dakatar da ayyukanta domin hadewa da na Ali Sherrif maganan kanzon kurege ne kawai amma bata da wata alfanu a garesu.

Adeyeye ya ce jami’yar PDP na bangaren Makarfi ba za ta dakatar da ayyukanta ba domin ba ita ta nada kanta ba.

Ya ce idan har dai yana so kwamitin ta dakatar da ayyukanta, toh kamata ya yi ya tuhumi manyan jam’iyyar wanda ya kunshi kashi 80 bisa 100 na mambobin jami’yyar wanda sune suka amince da nadin kwamitin Makarfin domin bata izinin dakatar da ayyukanta a madadin jam’iyyar PDP.

Ya ce da zaran sun amince da hakan za su dakatar da ayyukansu saboda kwamitinsu ba irin na Ali Modu Sheriff bane wanda ya ki amincewa da kiran da akayi ta masa da ya sauka daga kujeran shugabancin jam’iyyar domin samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin su duka.

Shugaban kwamitin sasantawa na bangarori biyu da basa ga maciji da juna na jami’yyar PDP kuma gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya yi kira ga jam’iyyar na bangaren Ahmed Makarfi da ta mai da wukan su rungumi sulhu domin cigaban jam’iyyar.

Seriake ya fadi hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce a halin da ake ciki jiga-jigan jam’iyyar na kokarin ganin cewa sun sasanta bangarorin biyu da kuma ganin cewa bangaren Makarfi ta dakatar da aiyukanta domin hadewa da bangaren Ali Modu Sheriff.

Ya ce a lokacin da aka amince wa Sheriff ya shugabanci jam’iyyar a wancan lokacin, yayi watsi da wannan shawara sannan ya nuna rashin amincewarsa akai amma tun da komai ya zama haka yanzu yana kira da rokon kowa ya mai da wukar nasa ya mara ma shi Sheriff baya domin a wuce in da ake yanzu.

Gwamnan ya kara da cewa a dalilin rashin jituwar bangarorin biyu yasa jam’iyyar na ta rasa wasu ‘ya’yanta in da suke tayin kaura zuwa wasu jam’iyyun kasannan.

Daga karshe ya roki bangaren Makarfi da su janye karar da suka shigar gaban kotun koli domin kalubalantar tabbatar wa Ali shugaban cin jam’iyyar da kotun daukaka kara tayi

Share.

game da Author