Wasu ‘yan fashi da makami sun kashe wasu ‘yan sanda biyu yayin da suke akin duba gari da safiyar ranar Litini a jihar Sokoto.
Kwamishinan rundunar ‘yan sandar jihar Muhammed Abdulkadir ya sanar wa manema labarai cewa ‘yan sandan sun yi anrangama da ‘yan fashin lokacin da suke kokarin bude ma’ajiyar kudi na gidan man NNPC dake Gusua a jihar Sokoto.
Abdulkadir yace ‘yan fashin sun yi fakon gidan man ne tun daga ranar Juma’a zuwa Lahadi.
Ya ce za su fadi sunayen ‘yan sanda da suka rasa rayukansu bayan sun tattauna da iyalensu.
Ya kuma ce sun kai gawawwakinsu dakin ajiye gawa na asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo dake Sokoto.
Bayan haka Abdulkadir ya kara tabbatar da tsintuwan wata gawa amma gangar jiki ce kawai domin an yanke kan gawar duk a ranar litinin din a buhu a wata bolar dake hanyar Maituta.
Daga karshe yace har wa yau babu wanda ‘yan sanda suka kama game da laifin kisan jami’an ta da aka kashe.