Hameed Ali ba zai je majalisa gobe ba

1

Shugaban hukumar kwastam Hameed Ali yace ba zai je majalisar dattijai goba kamar yadda majalisar ta bukace shi da yayi.

Kakakin hukumar kwastam Joseph Attah yace shugaban kwastam din ba zai samu damar halartar zauren majalisar ba saboda wata kara da wani mai suna Ibrahim ya shigar da kara kotu ya na neman kotun ta bashi bayanai akan ingancin tilasta wa Hameed Ali zuwa majalisar sanye da kayan hukumar Kwastam a dkar kasa Najeriya.

Ministan shari’a Abubakar malami ne ya rubuta wa Hameed Ali wasika da ya dakatar da zuwa majalisar saboda wannan kara da aka shigar wanda ya hada har dashi kansa Malami din.

Malami yace ofishinsa ta rubuta ma majalisar dattijai haka itama.

Wani tsohon janar a sojin Najeriya David Jemibewon, ya ce da shine majalisa ta bukaci ya saka Unifom din kwastam da sai dai ya ajiye aikin.

Janar David yace bai ga dalilin da zai sa wai ace maganar saka riga ya zama abin tada hankali ba.

” Ai nuna kaskanci ne ace wai tsohon soja da ya rike matsayi irin na Hameed Ali ya saka unifom irin na kwastam.

“Babu wani Wanda ya isa ya tilastani saka unifom a matsayina na tsohon janar a sojin Najeriya. Da inyi haka gara in ajiye aikin.

“Hameed Ali mutumin ne wanda ya yi aiki da samun yabo masu yawa a aikinsa. Ya koma ya saka kayan kwastam kuma ai ci baya ne.

Tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani Kayode ya musanta korafin Janar David in da ya ce ana shi ganin dole ne a Hameed Ali ya saka unifom kuma idan yaki a Kawo shi majalisa ko da cikin sarka ne zuwa majalisar.

Share.

game da Author