Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi tir da irin ɗanyen aikin kisa, garkuwa da ɓarnata dukiyar da ‘yan bindiga ke yi a faɗin ƙasar nan. Ya ce tilas ne duk wani ɗan bindiga a ɗauke shi matsayin ɗan ta’adda kawai.
Tinubu ya yi wannan iƙirarin a ranar Talata, lokacin da ya yi buɗe-baki da manyan alƙalai da manyan ma’aikatan shari’a, waɗanda suka kai ziyara Fadar Shugaban Ƙasa, a ƙarƙashin jagorancin Cif Jojin Najeriya, Olukoyede Ariwoola.
Shugaban ƙasar ya ƙara jaddada ƙoƙarin da gwamnatin sa ke yi wajen ganin ta daƙile ‘yan bindiga, ya na mai cewa duk mai yin garkuwa da ƙananan yara ba jarumi ba ne, matsoraci ne, kuma ya na jin tsoron yin gaba-da-gaba da sojojin Najeriya.
“Tilas sai fa mun yarda cewa su ma ‘yan bindiga ‘yan ta’adda ne, kuma a riƙa ragargazar su kamar yadda ake ragargazar ‘yan ta’adda, sannan za a iya shawo kan matsalar su.
“Matsoran banza ne kawai. Sojoji sun karya masu lago, shi ya sa su ke kai hare-hare a wuraren da babu tsaro su na garkuwa da ƙananan yara. Su na zuwa makarantu su na kama yara, su na haddasa jama’a cikin halin zullumi.
“Don haka tilas mu riƙe su matsayin ‘yan ta’adda idan har muna so mu kakkaɓe su daga cikin al’ummar mu.” Inji Tinubu
Discussion about this post