Naira ta fara ƙwatar wa kan ta martaba da daraja daga hannun Dala, yayin da aka sayar da ita Dala 1 kan Naira 1,382.95 a farashin gwamnati, a ranar Talata.
Kafin sannan dai ana sayar da Dala 2 Naira 1,408 ne a ranar Litinin.
Amma kuma hada-hadar masu zuba jari da masu fitar da kaya ƙasashen waje, an yi musayar Dala kan Naira 1,300 zuwa 1,489.
Idan ba a manta ba dai a ranar Talata ce Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙara wa masu karɓar lamuni a bankuna kuɗin ruwa, daga kashi 22.75 zuwa kashi 24.75.
Tun a ranar Juma’a ne dai Naira ta fara shaƙar numfashi, bayan Dala ta yi mata cin-kwalar-kuturun da ta sumar da ita.
Rahoton da wannan jarida ta buga a ranar Asabar, ya nuna yadda darajar Naira ta ɗan ɗaga sama inda a ranar Juma’a aka sayar da Dala 1 kan Naira 1,431.49.
Bayanan da suka fito daga Sashen Hada-hadar Kuɗaɗen Waje, sun nuna cewa darajar Naira ta ɗaga da ƙarfin Naira 21.79, wato ta ƙaru da kashi 1.5, idan aka kwatanta yadda aka sayar da Dala 1 kan Naira 1,453.28 kafin ranar Juma’a.
Amma a ɓangaren musayar kuɗaɗe ga masu zuba jari da masu fitar da kaya wajen Najeriya, an yi hada-hadar Dala kan Naira 1,468 da kuma 1,301.
Wannan jarida ta buga labarin cewa CBN ya raba Dalolin da ake bin sa bashin karɓa, ya ƙara yawan gejin kuɗaɗen asusun kuɗaɗen waje.
Babban Bankin Najeriya ya bayyana cewa babu sauran wani ko wasu masu bin sa bashin karɓar kuɗaɗen wajen da suke jiran karɓa, domin yin hada-hadar da Gwamnatin Najeriya ta amince su yi da kuɗaɗen.
Wannan yunƙuri da kuma ƙoƙari da dai Kakakin Yaɗa Labaran CBN ce, Hakama Sidi-Ali ta bayyana shi.
Discussion about this post