A jihar Kano jam’iyyar APC, na ci gaba da shirin rantsar da sabon gwamna nan ba da dadewa yayin da Jam’iyyar ke da yaƙinin cewa ɗan takarar jam’iyyar ne za a bayyana gwamnan jihar a hukuncin Kotun Koli da za a yanke ranar Juma’a mai zuwa.
Wakilin PREMIUM TIMES ya zagaya cikin garin Kano inda ya ga yadda ake ta rabon tirmin atamfa ga ƴaƴan jam’iyyar da magoya bayan jam’iyyar a faɗin jihar.
Tun a makon jiya jam’iyyar a Jihar Kano ta yi kira ga ƴaƴan ta su dunguma yin azumi da yankan dabbobi domin rokon Allah ya basu nasara a hukuncin da kotun zata yanke a ranar Juma’a.
An yi wa atamfar tambarin hular Tinubu gabaɗayanta, sannan ana rabata birni da ƙauye ga masoya da magoya baya don su ɗinka su saka ranar da za a bayyana hukuncin shari’ar zaɓen gwamnan da ranar rantsar da gwamna Nasiru Gawuna kamar yadda suke saka rai.
Faisal Ibrahim ya shida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa bisa ga hukuncin da kotunan baya suka yanke, yana da yakinin cewa Gawuna ne zai yi nasara a kotun Koli.
Haka kuma wasu da dama da suka znta da wakilin mu sun nuna kosawarsu suna masu ranar biki kawai suke jira, amma nasara kam ta su ce.
Jam’iyyar har ta raba goron gayyata da kullin alawa ga sauran magoya bayan jam’iyyar da ke makwabtaka da jihar Kano da ma sauran jihohin Arewa don halartar wanke Gawuna bayan yanke hukunci ranar Juma’a.
Discussion about this post