Kotun ƙoli ta bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin ƙarshe kan shari’ar gwamnan Kano tsakanin gwamna Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC.
Jagoran Alkalai biyar da suka saurari lauyoyin masu kara da waɗanda ake kare wa Alkali Okoro ya ce bayan sauraren jawaban lauyoyin kowanni ɓangare.
Yusuf na jam’iyyar NNPP ya shigar da ƙara kotun koli domin ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zaɓe da ta soke nasararsa tare da bayyana Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
Daga nan sai Okoro ya buƙaci ɓangarorin da ke cikin shari’ar su samu matsaya kan ɗaya daga cikin ƙorafe-ƙorafe tara da aka ɗaukaka ƙara a kai, wanda hukuncin da za a yanke kan sa zai shafi sauran ƙorafe-ƙorafen takwas.
Daga nan ne aka cimma matsaya kan cewa ƙorafin da za a saurara shi ne wanda ake ƙalubalantar kasancewar gwamna Yusuf ɗan jam’iyyar NNPP ne ko kuma ba ɗan jam’aiyyar bane.
Mai kare gwamna Yusuf, Wale Olanipekun ya shaida wa kotu cewa ita kanta kotun Koli ta taba yanke hukunci irin haka da ake ƙalubalantar zaman wani ɗan takara ba ɗan jam’aiyya bane.
” Tun farko jam’iyyar APC bata ƙalubalanci rashin zaman Yusuf ɗan jam’aiyyar APC ba har sai da aka yi zaɓe. Sannan kuma Kotu ba ta da damar ta tsige gwamna da aka zaɓa a dalilin zaman sa ɗan jam’iyya ko kuma ba ɗan jam’iyya ba. Wannan hurumi ne na kotu ba.
Olanipekun ya bayar da wasu hujjoji da ita kanta kotun koli ta yi amfani da su wajen yanke irin wannan hukunci a baya, da ke nuna ba matsala bane. ” Sannan kuma ita kanta kotun ta ce wata jam’iyya bata da hurumin bincikar matsayin ɗan takarar wani jam’iyya.
A karshe shima lauya mai kare hukumar Zaɓe, Mahmood ya tabbatar wa kotun Koli cewa duka takardun zaɓen da aka yi amfani da su a Kano na hukumar ne babu na boge.
Discussion about this post