Jigo a kwamitin dattawan Kaduna Mohammed Rabiu Bako, ya jaddada cewa kasafin kudi na 2024 wanda gwamnan Kaduna Uba Sani ya gabatar a majalisar jihar ranar Litinin zai gyara kura-kuran da gwamnatin Nasiru El-Rufai ya tafka shekaru8 da suka gabata.
A wata jawabi da ya fitar a garin Kaduna, Dattijo Rabiu-Bako ya shaida cewa Kasafin Kudin ya yi daidai da halain da ake ciki da jihar, kuma kasafin zai gyara kurakuran da gwamnatin Nasir El-Rufai ya tafka a zamani sa.
“Gwamnatin da ta shude, sam bata kula da karkara da mutanen karkara ba. Gaba daya an fi maida hankali ne wajen kawata babban birnin Kaduna, an wancakalar da karkara da mutanen ta. Amma wannan kasafi wanda gwamna Sani ya gabatar zai fi maida hankali ne ga ayyukan raya karkara.
” Hakan da gwamna Sani yayi ya nuna cewa lallai gwamnan da gaske ya ke yi don gina kananan hukumomin jihar da kuma mutanen karkara sabanin gwamnatin baya da babu abinda ya dadata da kasa game da kauyukan mu.
” Sannan kuma idan muka kula da yadda ya somo tafiyar sa musammam wajen bangaren tsaro, za ku ga cewa tafiyar ta kowa da kowa ce sabanin irin yadda gwamnatin El-Rufai ta yi nata, ‘gwamnatin shafaffu da mai kawai’.
Discussion about this post