Dan takatar gwamna Kogi na SDP, Murtala Ajaka ya yi ikirarin cewa an hada baki da hukumar zabe an yi masa rinto a zaben gwamna da aka yi Kogi ranar Asabar.
A wata hira da ya yi da talbijin din Channels, Ajaka ya ce ba zabe aka yi a Kogi ba , dauki dora aka yi kawai domin irin kuri’un da aka rika fiddo wa daga wasu kananan hukumomin jihar hankali ma ba zai dauka ba.
” Kamar Karanmar hukumar Okene, ace wai an fiddo kuri’u sama da 130,000, daga ina aka same su. Sannan kuma a kundin IReV mutum 30,000 ne kawai suka kada kuri’a. Amma INEC da yi gaban kanta ta bayyana sakamakon zaben haka.
” Idan shugaban hukumar zabe bai duba wannan abu da ya faru a Kogi ba ya bari a ka cigaba a haka to, a 2027, za a yi kare jini biri jini ne a zabe, don mutane za su fito ne shirye da makaman su. Sai an ce abinda aka yi a Somaliya wasan yara ne.
” Muma da mun sani cewa ashe duk kanwar ja ce, da tun da wuri mun rika lafta aringizon kuri’un karya a yankunan mu daon mu samu kuri’u, amma sai muka bari saboda mun yarda da INEC za ta yi gaskiya, ga shi yanzu mun kwan ciki.
“Kun ba ni tabbacin cewa za a yi zabe cikin gaskiya, amma kawai kun bari na ba’ta lokaci na a banza, na kashe kudade ne a banza, na ba’ta wa mutane lokaci a banza tsammanin INEC za ta yi gaskiya a zaben Kogi.
Discussion about this post