Kungiyar Kwadago ta Kasa ta umarci duka kungiyoyin ta na jihohi da kungiyoyin ma’aikata sun tsindima yajin aiki daga ranar Talata.
Idan ba a manta ba tun bayan mauje shugaban Jam’iyyar da ‘yan sanda suka yia jihar Imo, Kungiyar ta bayyana cewa za ta fara yajin aiki domin ramako ko abinda aka yi wa shugabanta a imo.
Sai dai kuma wata kotu ta hana kungiyar aiwatar da wannan yajin aiki a hukuncin da ta yanke a makon jiya.
Da alama dai wannan hukunci ba zai yi tasiri ba domin kungiyar kwadagon ta umarci dukkannin kungiyoyin dake karkashinta su fara shirin tsindima yajin aiki gadan-gadan daga ranar Talata.
NLC da TUC sun umarci dukkan ma’aikata a Najeriya da su dakatar da ayyukansu daga karfe 12:00 na daren yau, 13 ga Nuwamba, 2023.
Discussion about this post