Kotun Ɗaukaka Ƙara ta fito a ranar Laraba ta bayyana cewa an tafka kuskure wajen buga sakamakon hukuncin shari’ar zaɓen Kano, inda a cikin kundin bayanin shari’ar, aka buga cewa Gwamna Abba Yusuf ne ya yi nasara.
Babban Rajista na Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, Mista Bangari ne bayyana haka a ranar Alhamis.
Ya ce kuskuren da aka tafka ɗin ba zai zama ya shafe hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a ranar 17 ga Nuwamba ba.
Haka Bangari ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Sannan kuma ya ce Kotun Ɗaukaka Ƙara za ta gyara tuntuɓen alƙalamin wanda aka yi da zarar lauyoyin ɓangarorin biyu sun maido kwafen da aka damƙa masu, domin a yi gyara.
A na ta ɓangaren kuwa, Gwamnatin Kano ta bakin Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na jihar, ya ce ‘kwafen hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ya tabbatar da Abba Gida-gida ne kotun ta bai wa nasara.’
Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Haruna Isa-Dederi, ya bayyana cewa Kwafen hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja ta fitar ya tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir-Yusuf na NNPP ne ya lashe zaɓen Kano.
Haruna Dederi ya bayyana hakan a wata ganawar da ya yi da manema labarai, ranar Talata a Kano.
Dederi ya faɗi haka, yayin da wani kwafen da kotun ta fitar, inda ta jingine hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Kano ta bayyana cewa Abba bai cancanta ba, don haka Nasiru Yusuf na APC ya yi nasara.
Kwafen ya ce ƙarar da APC ta shigar ba ta wani hurumi.
“Hujja a cikin shafi na 67 na kwafen hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta zartas kuma ta fitar a ranar Talata, mai ɗauke da sa hannun Rajistara na Kotun Ɗaukaka Ƙara, Jameel Ibrahim Umar, ya tabbatar da cewa ta jaddada nasarar da Abba ya yi a zaɓen Kano.” Haka Dederi ya bayyana.
Duk da cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce Nasiru Gawuna ne ya yi nasara, amma kuma a shafi na 67 na kwafen hukuncin ya nuna cewa kotun ta jingine hukuncin da kotun Kano ta soke zaɓen Abba.
Dederi ya ce kwafen hukuncin ya saɓa da abin da alƙalan suka karanta a lokacin yanke hukunci, a Abuja, a ranar 17 ga Nuwamba.
Dederi ya ce wannan abu da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta fitar kuma ta damƙa masu a rubuce, zai ƙara masu ƙwarin guiwa a Kotun Ƙoli.
Discussion about this post