Kakakin Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya ƙaryata zargin ana karkatar da haƙƙin kuɗaɗen alawus-alawus na sojojin da ke tsaron wasu ‘yan Chana da ke aikin Madatsar Ruwan Samar da Wutar Lantarki a Zungeru da ke Jihar Neja.
Burgediya Janar Nwachukwu ya yi wannan raddi a ranar Litinin a Abuja, biyo bayan wani rahoto da wasu kafafen yaɗa labarai suka wallafa.
Ya tabbatar da cewa waɗanda suka buga labaran zargin Babban Kwamandan Runduna, Janar Bamidele Alabi da Burgediya Janar Jamiu Jimoh ba su biya su kuɗaɗen alawus ɗin ‘RCA’ na watanni uku ba, to ba gaskiya ba ce.
“Ba kamar yadda aka riƙa suka da tsangwama a wasu rahotonni cewa an riƙe kuɗaɗen alawus-alawus na wasu dakarun da aka kirge su na tsaron lafiyar ‘yan Chana masu aiki a Tashar Madatsar Ruwan Zungeru ba, to gaskiya alawus ya na zuwa ne a tsitstsinke, kuma ana ba su a duk lokacin da ya zo daga hukumar da lamarin biyan ke hannun ta.
“Biyan alawus na ƙarshe da aka yi wa dakarun shi ne na ranar 28 ga Fabrairu.
“To kuma ana nan ana tsare-tsaren sake biyan wasu kuɗaɗen alawus ɗin kwanan nan.
“Hedikwatar Sojojin Najeriya kuma ta biya dakarun wani alawus na watan Maris da Yuni, saboda kula da irin halin da suke ciki, saboda an girke su can wani wuri daban.
“Sannan kuma, domin magance matsalar yadda alawus-alawus na su ke zuwa a tsitstsinka, sai ake ciyar da su a kowace rana, ba tare da sai sun yi ta jiran tsammanin zuwan alawus-alawus na su ba, a kowace rana.
“Saboda haka alawus-alawus ɗin ‘RCA’ dai ba wanda ya karkatar da shi, ballantana a buga sunayen wasu a ce wai su ɗin ne su ka karkatar da kuɗaɗen.”
Haka Burgediya Janar Nwachukwu ya ci gaba da nanatawa a cikin sanarwar da ya fitar.
Ya ce yayin da Mahukuntan Sojojin Najeriya suka fahimci irin damuwar da aka nuna a cikin zarge-zargen, to kuma da a sani cewa Sojojin Najeriya a ƙarƙashin Laftanar Taoreed Lagbaja, sun tsaya haiƙan wajen kula da jin daɗin dakarun ƙasar nan.
Discussion about this post