Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince siyan jiragen yaki masu saukar ungulu 12 ga sojojin Najeriya.
Babban Hafsan Sojojin Najeriya Taoreed Lagbaja, ya bayyana haka a wajen bude taron koli na Sojojin Najeriya, ranar Talata a Abuja.
Yace wadannan Jirage za su rika aiki ne domin taimakawa sojojin Kasa a lokacin da suka kai farmaki wa ‘yan ta’adda a dazuka.
Sannan kuma za su taimaka wajen aikin samar da tsaro da sojojin Najeriya ke yi a fadin kasar nan.
” Tun 2014 rundunar sojin Najeriya ta maida hankali wajen horas da matukan jirgi, injiniyoyin jiragen sama,kwararru da sauran ma’aikatan jirgin ruwa,”
Wannan bangare ne na mayakan sama dake karkashin rundunar sojin Najeriya.
Discussion about this post