Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji, FIRS ta bayyana cewa ta shirya fito da sabon tsarin amsar haraji daga hannun ‘yan tireda masu kananan sana’o’i.
Za a samu nasarar wannan tsari ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar ‘yan tireda da FIRS, ta hanyar tsarin fasahar zamani.
Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin, ta ce Shugaban FIRS, Muhammad Name, ya ce za a yi kwamiti wanda za ya haɗa da jami’an FlRS da na MATAN nan ba da daɗewa ba
Sannan ya ce za a yi tsarin ta yadda za a toshe hanyoyin ciwa-cewa da harƙalla.
Sanarwar ta ce MATAN na da mambobi sama da miliyan 40 na ‘yan tireda a faɗin ƙasar nan
Za bayar da shedar zama mamba, da kuma tsarin tabbatar da ana amsar harajin.
Daga nan ya ce tsarin zai magance matsalolin ‘yan daba masu wuru-wurun kuɗaɗe.
Wannan tsari na karɓar harajin ‘VAT’ daga hannun ‘yan tireda masu samu da kyar, ci da kyar, zai samar da yawan kuɗaɗen shiga ga Gwamnatin Tarayya har zuwa jihohi da ƙananan hukumomi.
Discussion about this post