Sakamakon wani bincike da (Tap Nitiative for Citizens Development da Dataphyte) suka gudanar kan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 30 dake Babban Birnin Tarayya Abuja ya bankado muhimman matsalolin da cibiyoyin ke fama da su da ya kamata a yi gaggawan kawar da su.
Binciken ya nuna cewa cibiyoyin lafiya 18 daga cikin 30 din dake Abuja na fama da karancin ma’aikatan lafiya, 21 na fama da rashin kwararrun masana magunguna, 14 ba su da masu bada kati, 12 basu da dakin yin gwaji sannan daya ne kadai ke da ma’aikacin ma’aji.
Wadannan matsaloli da bincike ya gano na daga cikin matsalolin dake kawo cikas a harkar samar da kiwon lafiya a Abuja kamr yadda bincike ya gano.
Binciken ya kuma gano cewa cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare tsakanin ma’aikatan cibiyoyin.
Cin hanci da rashawa na daga cikin matsalolin dake hana mutane zuwa asibiti tare da hana asibitocin samun kwararrun ma’aikata.
Bayan haka kashi 81 cikin 100 sun bayyana cewa ba su risit din biyan kudi magani a asibiti.
Kashi 7.5% sun Kuma koka da yadda basa samun gamsuwa idan sun je asibiti saboda tsananin cin hanci da rashawa da ya yi wa ma’aikatan rawani. Da yawa sun ce sai sun bada cin hanci kafin a duba su tukunna.
Sannan kuma akalla kashi 78 cikin 100 na masu zuwa asibitocin ba su san irin abubuwan da ake iya samu kyauta a cibiyoyin ba kamar mafani ƙanjamau da dai sauran su.
Hanyoyin da za su taimaka waken inganta cibiyoyin lafiya na matakin farko a Abuja.
1. Ya kamata gwamnati ta dauki kwararrun ma’aikata musamman a cibiyoyin lafiya na matakin farko 18 a Abuja.
2. Daukan matakai domin hana cin hanci da rashawa a asibitocin.
3. A tabbatar cewa ma’aikatan asibiti na Bai wa mutane takardan shaidan duk kudaden da mutane suka biya a asibiti domin hana ma’aikatan yin sama da fadi da kudaden asibitin.
Discussion about this post