APC ta bayyana cewa ba da shawarar ta da amcewar ta Dattawa suka naɗa Shugabanni ba.
Shugaban APC Abdullahi Adamu ne ya bayyana haka taron da APC ta yi da Gwamnonin ta, ranar Talata, a Abuja.
Ya ce babu hannun APC, ba a wanda ya yi shawara da shugabannin ta.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Sanata Ndume ya zama Bulaliyar Majalisar Dattawa, Umuahi Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye.
An zaɓi tsohon Gwamnan Ebonyi, Sanata Dave Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, yayin da Sanata Ndume daga Jihar Barno ya zama Bulaliyar Majalisar Dattawa.
Sanata Lola Mataimakin Bulalar Majalisa.
An amince da su ba tare da wata jayayya ba, a matsayin waɗanda jam’yyar APC ta amince da su.
An zaɓe su wata ɗaya bayan Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin kuma mataimakin sa.
Sabuwar Majalisar Dattawa ta 10 ta zaɓi Sanata Godswill Akpabio daga jihar Akwa Ibom sabon Shugaban Majalisar Dattawa.
Sanata Barau Jibrin daga Jihar Kano aka zaɓa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Akpabio ya fito daga Kudu maso Gabas, shi kuma Barau Jibrin daga Arewa maso Yamma.
Akpabio ya kayar da Sanata Abdul’aziz Yari daga Jihar Zamfara, inda ya samu ƙuri’u 63, shi kuma Yari 46.
an fara zaɓe tun ƙarfe 8:45 na safe, a Zauren Majalisar Dattawa, wanda nan da nan aka rantsar da Akpabio bayan an zaɓe shi.
Akpabio shi ne Shugaban Majalisar Dattawa na 9, bayan dawowar dimokraɗiyya wato a Jamhuriya ta Huɗu.
Sanata Barau Jibrin ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ba tare da samun mai hamayya ba.
Sanata David Umahi da Sanata Sani Mustapha na Jihar Kwara ne su ka nemi a zaɓe shi, kuma aka amince.
Akpabio tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom ne, wanda bayan saukar sa cikin 2015 a ƙarshen mulkin Goodluck Jonathan, aka zarge shi da wawure Naira biliyan 102.
Discussion about this post