Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayyana cewa ko tantama ba yayi game da jarumtakar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a fagen siyasar Najeriya.
” Amma fa jarumtar sa a fagen yin takara ne da kuma faɗi zaɓe. Shike nan bai wuce haka kuma shima ya sani mu ba sa’o’in sa bane, tuni mun yi gaba na baya sai tsintar hula.
Masari a cikin hira da yayi wanda PREMIUM TIMES Hausa ta ci karo da, ya kara da cewa lokaci yayi da mutanen Katsina za su saka wa Bola Tinubu bisa biyayyar da ya yi Buhari ɗan asalin jihar.
” Idan ka duba, a 2015, Tinubun nan ya baiwa Buhari goyon baya ɗari bisa ɗari, haka kuma a 2019, ya yi irin haka, Saboda haka sunansa ba biyayya bace a jigar Katsina.
Da aka tambayeshi game da goguwar Peter Obi da ta darkako, Masari ya ba da amasar cewa, ” Wanene Peter Obi, ana maganar Najeriya ka kawo mana wani Peter Obi. Ai ruwa ba tsarar kwando bane.
” Ka shiga garin Katsina ka tambayi wani ɗan siyasa ko wanene Peter Obi? Nan ne za ka san ba kowan komai bane, don a nan ba a san shi ba. Amma Tinubu ko ina an san shi kuma an sa irin gudunmawar da ya baiwa jihar.
Discussion about this post