Masu tuƙa baburan Keke NAPEP a jihar Kaduna sun koka kan yawan kudaden da suke biya wa gwamnati ta hannun kungiyoyin karbar haraji a jihar.
Ƴan Keke NAPEP sun yi kira ga gwamnati ta saka baki cikin al’amarin domin rage yawan harajin da suke biya.
Wani dan keke mai suna David Akin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Najeriya a garin Kaduna cewa, a unguwar Sabon Tasha kawai masu karbar kudin haraji a hannun su sun kai biyar.
Akin ya ce ya yi lissafin yana kashe naira 2,500 duk rana kawai wajen biyan kudin haraji a unguwar Sabon Tasha dake Kaduna.
“Garin Allah na wayewa za ka hadu da matasa daga kungiyoyin karban haraji daban-daban sannan ba su da mutunci ko ka biya ne ko kuma su gurza maka rashin mutunci.
“Zan so da gwamnati ta rusa duk kungiyoyin ta kafa guda daya kawai zai rika karban harajin.
Haka shima Yusuf Nda dake aiki Keke a Ungwan Rimi ya koka kan irin yadda ake karbar haraji a hannun su.
“Za ka hadu da wadanda za su karbi Naira 100, 1,000 ko 4,000 kudin fenti, tikiti ko sitika.
“A dalilin hakan ya sa muke kara kudin mota Amma muna kira ga gwamnati da ta nema mana mafita.
Danlami Yunisa dake aiki Keke a Narayi ya ce a dalilin harajin da suke biya wasu da suka karbi hayan Keke basu iya biyan kudin hayan da ya kamata su biya.
“Sannan gashi wasu masu hayan Keke basu so su ji cewa kudinsu ya shiga cikin kudin biyan haraji su dai kudin su kawai suke so.
Discussion about this post