Sanata Dino Melaye ya gargaɗi ɗan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu da illahirin magoya bayan sa da ita kanta Jam’íyyar APC din sukutum da su daina cika baki domin ruwa ba tsarar kwando bane.
Dino ya ce ” Inda Katafila ke shawagi ba wuri bane na mota ‘Kumbirin Dinka’ domin idan ya shiga wannan fage, murƙusheshi za a yi. Haka takarar Atiku ya ke da Tinubu. Murƙushe Tinubu Atiku zai yi cikin ruwan sanyi a zaɓen 2023.
Dino ya ƙara da cewa su a PDP tuni har sun gaya wa ɗan takarar su ya rubuta jawabin samun nasara tun yanzu domin lokaci kawai a ke jira.
A wannan hira da yayi da talbijin ɗin Channels dino ya rika yin kumfar baki naya kuri, yana zazzaro idanu yana wasa ɗan takarar sa, Atiku Abubakar.
” Mu fa a jam’iyyar PDP, mun gaya wa ɗan takarar mu Atiku Abubakar, ya rubuta jawabin murnar yin nasara a zaɓen shugaban kasa domin tun 11:30 na safe za mu barke da buki bayan zaɓen 2023.
” Ku duba yadda Tinubu yake, ba shi da karfi a jika, ba shi da koshin lafiya sannan ga tsufa. Shikenan za mu sake komawa gidan jiya ne bayan bamu gama da wanda yake akai ba yanzu.
” Atiku duk da shekarun sa ya fi Tinubu lafiya. Ko a jiya sai da ya murza tamola a gidan sa. Lafiya lau amma ku duba Tinubu ku gani mana.