Akalla mutum 113 ne ‘yan bindiga suka kashe daga ranar 5 zuwa 11 ga Yunin 2022 a kasar nan.
Bisa ga alkaluman da aka fitar ya nuna cewa an samu karin mutum sama da kashi 50% da aka kashe a daga makon jiya zuwa wannan mako.
A makon jiya ƴan bindiga sun kashe mutum 48.
Mahara sun kashe wadannan mutane a shiyoyi hudu daga cikin shiyoyi shida na kasar nan.
Daga ciki akwai kisan gillar da aka yi wa mutane a coci dake Owo a jihar Ondo inda aka kashe mutum 40.
PREMIUM TIMES ta samu alkaluman yawan mutanen da aka kashe daga rahotannin da gidajen jaridu suka buga
Kudu maso Yamma
Akalla mutum 40 ne ‘yan bindiga suka kashe a Cocin Katolika na St Francis dake kauyen Owo jihar Ondo ranar Lahadin da ya gabata.
Mutane da dama da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari sun yi alhinin kisan da aka yi wa masu bautan.
Bayan haka a ranar Laraban da ya gabata ‘yan bindiga sun kashe mutum shida a Sabo dake jihar.
An yi jana’izar mutanen da suka mutu a ranar Laraba sannan wadanda suka ji rauni na samun kula a asibiti.
Arewa maso Yamma
A ranar Asabar din makon jiya ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan dake Gebe da Alkammu a karamar hukumar Isa, jihar Sokoto.
Maharan sun kashe matar dagacen sannan suka yi garkuwa da mutum 57 daga kauyukan.
A jihar Kaduna mahara sun kashe mutum 32 a kauyukan Ungwan Gamu, Dogon Noma, Ungwan Sarki da Maikori dake karamar hukumar Kajuru.
Kungiyar kabilar Adara ta ce maharan sun afka wa kauyukan ranar Lahadi da misalin karfe 12 na rana sukanyi ta tabargaza har zuwa karfe shida na yamma.
Arewa ta Tsakiya
A jihar Kwara ‘yan bindiga sun kashe mutum biyu yayin da suke kokarin yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Ekiti.
Kakakin rundunar Okasanmi Ajayi wanda ya sanar da haka ranar Lahadi ya ce maharan sun tare motar hanyar Obbo-Aiyegunle-Osi ranar Asabar.
A gundumar Kuje dake babban birnin tarayya Abuja wasu Fulani makiyaya sun kashe wani manomi Hussaini Takuma sannan suka jefa gawar mutumin a cikin rijiya.
Makiyayan sun saci shanu 30, da tumakai 20.
Kudu maso Gabas
A jihar Anambra ‘yan bindiga sun kashe shugaban matasa na Jam’iyyar APGA Emeka Alaehobi a kauyen Utuh dake karamar hukumar Nnewi ta Kudu.
Maharan sun yi garkuwa da Alaehobi a gidan sa dake kauyen Upor ranar Alhamis din wannan mako.
Discussion about this post