Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana wani iƙirari da Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi cewar wai jami’an gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa sun sace naira biliyan 1 “a kan idon Shugaba Muhammadu Buhari” na Shirin Tallafin Rage Fatara (SIP) wanda ma’aikatar ke gudanarwa da cewar ƙarya ce maras makama.
Wasu kafafen yaɗa labarai sun kuma ruwaito gwamnan ya na faɗin cewa “cin hanci da rashawa ya riga ya ruguza shirin tallafin NSIP na Gwamnatin Tarayya, sannan ya ƙalubalanci gwamnatin da ta kwaikwayi sabon shirin da gwamnatin sa ta ke aiwatarwa a Jihar Bauchi.
Ya yi maganar ne a wajen taron ƙaddamar da shiri mai suna ‘Ƙaura Economic Empowerment Programme’ (KEEP).
Haka kuma gwamnan ya ce, “A yau, shirin tallafa wa jama’a ya rushe domin a yanzu babu wanda ke samun komai daga gare shi.”
To amma a martanin da ta yi masa, ma’aikatar ta bayyana cewa maganganun gwamnan ba su da wata hujja, “ƙarya ce ƙarara, kuma ba su da wata alƙibla ko kaɗan idan an duba gaskiyar abin da ake yi a shirin.”
A cikin wata sanarwa da Jagoran Shirin Tallafin Rage Fatara na Ƙasa (NSIP), Dakta Umar B. Bindir, ya rattaba wa hannu, ya ce: “Shirin Tallafin Rage Fatara na Ƙasa (NSIP) na Gwamnatin Tarayya, wanda mai girma Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar a cikin 2016, kuma a yanzu ya ke ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, ya na nan daram daƙam, ana ci gaba da shi, da ƙarfin sa, sannan ya na ƙara faɗaɗa ya na isa ga jama’a kuma ya na kawo kyakkyawan tasiri a rayuwar talakawa marasa galihu da ke amfana da shi a faɗin ƙasar nan, ciki har da Jihar Bauchi.
“Duk wanda ya ce ba haka ba ne, to bai san gaskiyar abin da ke faruwa ba wajen aiwatar da shirin na NSIP a jihar sa musamman, kamar yadda ake ta bada rahotanni a kafafen yaɗa labarai irin na da da kuma na zamani.”
Dakta Bindir, wanda injiniya ne, ya ƙara da cewa: “Mu na nanata cewa Shirin Tallafin Rage Fatara na Ƙasa (NSIP), duk da yake Gwamnatin Tarayya ce ke ɗaukar nauyin sa kacokam, ana aiwatar da shi ne ɗari bisa ɗari tare da haɗin gwiwar jami’an gwamnatin jiha da mutane ‘yan asalin jihar, waɗanda ke aiki ba tare da gajiyawa ba tare da ma’aikatan NSIP da su ka zo daga Gwammatin Tarayya domin isar da alfanun da ke cikin tsare-tsaren shirin ga talakawa da sauran marasa galihu a jihohin da su ke, bisa kyakkyawar niyyar mai girma Shugaban Ƙasa ta ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara da yunwa ya zuwa shekara ta 2030.
“Shugaban kwamitin aiwatar da shirin na NSIP na jiha mutum ne wanda mai girma Gwamna ya naɗa da kan shi.
“Dukkan masu cin gajiyar shirin da waɗanda su ke da hannu cikin dukkan tsare-tsaren shirin ‘yan asalin jihar ne, haka kuma ana biyan kowa kai-tsaye a cikin asusun sa na banki.”
Bugu da ƙari, ya bada misalai na yadda al’ummar Jihar Bauchi su ke amfana daga waɗannan tsare-tsare na rage fatara na Gwamnatin Tarayya kamar haka:
“a) A shirin musamnan na ciyarwa a makarantu na ƙasa, wato ‘National Home-Grown School Feeding Programme’ (NHGSFP), ana biyan dukkan masu dafa abinci, waɗanda dukkan su gwamnatin jihar ce ta zaɓo su ta ɗauke su aiki, kai-tsaye a asusun su na banki.
“Haka ma jami’an da ke duba kayan abinci, dukkan su mai girma Gwamna ne ya zaɓo su da kan shi ya gabatar da su ga Ma’aikatar, kuma su ma kowannen su ana biyan sa ne kai-tsaye a asusun sa na banki.
“A Jihar Bauchi, akwai makarantun firamare guda 3,357 (dubu uku da ɗari uku da hamsin da bakwai) waɗanda su ka ƙunshi ɗalibai 444,099 (dubu ɗari huɗu da arba’in da huɗu da casa’in da tara), da masu dafa abinci 7,538 (dubu bakwai da ɗari biyar da talatin da takwas), da masu duba kayan abinci su 12 (goma sha biyu) da ke aiki a cikin shirin ciyarwa a makarantu na ƙasa, wato ‘National Home-Grown School Feeding Programme’.
“b) Ana biyan masu cin moriyar shirin ‘N-Power’, waɗanda dukkan su ‘yan asalin jihar ne, kai-tsaye a asusun su na banki. Waɗannan ma’aikata na ‘N-Power’ an jona su ne da makarantu da asibitoci da cibiyoyin shirin aikin gona da ke faɗin jihar. A ƙarƙashin Rukunin ‘A’ na shirin, mutanen da su ka gama jami’a su 4,837 (dubu huɗu da ɗari takwas da talatin da bakwai) ne su ka amfana, a Rukunin ‘B’ kuma mutanen da su ka gama jami’a su 8,041 (dubu takwas da arba’in da ɗaya) sun amfana, yayin da matasa da ba su gama jami’a ba su 1,667 (dubu ɗaya da ɗari shida da sittin da bakwai) su ma sun amfana a ƙarƙashin tsarin ‘N-Build’, sannan mutum 339 (ɗari uku da talatin da tara) su ka amfana da shirin ‘N-Knowledge’.
“Yanzu haka, a ƙarƙashin Rukunin ‘C1’, akwai matasa da su ka gama jami’a su 14,535 (dubu goma sha huɗu da ɗari biyar da talatin da biyar), da mutum 629 (ɗari shida da ashirin da tara) da ke amfana da shirin ‘N-Knowledge’, da mutum 301 (ɗari uku da ɗaya) waɗanda aka ɗauka a ƙarƙashin tsarin ‘Mobile Money Agents’ da mutum 175 (ɗari da saba’in da biyar) waɗanda aka ɗauka a shirin koyon gyaran waya duk a Jihar Bauchi.
“c) A ƙarƙashin shirin nan na gwamnati na bada tallafin yin sana’a mai suna ‘Government Enterprise and Empowerment Programme’ (GEEP), ana biyan dukkan masu cin moriyar shirin rancen kuɗi kai-tsaye a asusun su na banki ba tare da sun biya kuɗin ruwa ko bada kadarar tabbaci ba, wato ‘collateral’. A Jihar Bauchi, a shirin GEEP 2.0 har an yi wa jimillar mutum 37,907 (dubu talatin da bakwai da ɗari tara da bakwai) daga dukkan Yankunan Ƙananan Hukumomi guda 20 na jihar rajista domin su shiga tsare-tsaren tallafi na MarketMoni, TraderMoni da FarmerMoni.
“d) A tsarin tura tsabar kuɗi na ‘Conditional Cash Transfer’ (CCT), an gano dukkan gidajen marasa galihu kuma an saka su cikin Rajistar Al’umma ta Ƙasa, ‘National Social Register’ (NSR) ta hanyar wani tsari mai zaman kan sa da ake kira ‘Community Based Targeting’ (CBT) a kowace jiha. An samar da rajistar ne daga rajistar da ke kowace jiha wadda akwai ta a Ma’aikatar Tsare-tsare ta jiha, ciki kuwa har da Jihar Bauchi.
“Daga wannan rajistar ta ƙasa baki ɗaya ne ake zaɓar waɗanda ke cin moriyar shirin na ‘Conditional Cash Transfer’ sannan a saka su a cikin Rajistar Masu Cin Moriyar Shiri ta Ƙasa, ‘National Beneficiary Register’ (NBR), wadda ake amfani da ita ana biyan kuɗi N5,000 (naira dubu biyar) ga kowane mutum a duk wata har na tsawon sama da shekara biyu.
“A Jihar Bauchi, akwai gidajen marasa galihu guda 75,110 (dubu saba’in da biyar da ɗari ɗaya da goma) waɗanda ke cikin wannan tsari, kuma sun ƙunshi mutum 401,395 (dubu ɗari huɗu da ɗaya, da ɗari uku da casa’in da biyar), kuma daga cikin su an samu jimillar mutum 99,957 (dubu casa’in da tara da ɗari tara da hansin da bakwai) daga Yankunan Ƙananan Hukumomi 20 waɗanda sun shiga rajistar ƙasa baki ɗaya, ana biyan su a kowane wata babu fashi.
“e) Shirin musamman na tallafa wa matan karkara, wato ‘Grant for Rural Women’ wani tsari ne da mai girma Shugaban Ƙasa ya amince da shi inda ake tallafa wa matan karkara da mata marasa galihu ta hanyar ba kowaccen su kyautar kuɗi N20,000 (naira dubu ashirin) biya ɗaya da nufin ba su damar su ja jarin yin sana’a, musamman ma domin su riƙa samun kuɗin shiga.
“A Jihar Bauchi, jimillar mata 8,671 (dubu takwas da ɗari shida da saba’in da ɗaya), waɗanda dukkan su ‘yan asalin jihar ne, sun shiga shirin.
“f) An ɗauki ma’aikata ‘yan sa ido kan shirye-shiryen bada tallafi, wato ‘Independent Monitors’, waɗanda duk ‘yan asalin jihar ne, don tabbatar da cewa an aiwatar da shirin tallafi na NSIP ba tare da wata ƙumbiya-ƙumbiya ba.
“A Jihar Bauchi, jimillar ma’aikata ‘yan sa ido guda 268 (ɗari biyu da sittin da takwas) aka ɗauka daga dukkan Ƙananan Hukumomi 20 na jihar, kuma ana biyan kowannen su alawus ɗin N30,000 (naira dubu talatin) a kowane wata a cikin asusun sa na banki.
“g) An kafa cibiyoyin kimiyya da fasaha da lissafi (Science Technology Engineering and Mathematics, STEM) da kayan aiki da ake buƙata a wasu zaɓaɓɓun makarantun sakandare na kimiyya da nufin bada nagartaccen ilimin kimiyya, aikin injiniya da fasaha, sannan a samar da ƙwarewa a fannin hanyoyin sadarwa na zamani ga ɗalibai.
“A Jihar Bauchi, a yanzu akwai irin waɗannan cibiyoyin na STEM guda 13 (sha uku) waɗanda ke aiki, kuma an tanadar masu da kayan aiki, har ma an ɗauki ma’aikata guda 3 (uku) waɗanda aka horar kan ilimin STEM aka tura su a kowace daga cikin makarantun.
“h) Yanzu haka ana aiwatar da shirin karantarwa na musamman wanda ake kira ‘Alternate School Programme’, ASP) wanda ake so a horas da yaran da ba su zuwa makaranta guda 1,000,000 (miliyan ɗaya) a duk faɗin ƙasar nan kamar yadda mai girma Shugaban Ƙasa ya aminta. Jihar Bauchi na cikin shirin tsindum, kamar dai dukkan sauran jihohin ƙasar nan.”
A cewar Dakta Bindir, “Waɗannan bayyanannun hujjojin da aka lissafa a sama sun isa su bada cikakkiyar shaidar cewa shirin tallafin rage fatara da yunwa na ƙasa (NSIP) ya na aiki sosai a dukkan faɗin Nijeriya, har da Jihar Bauchi.”
Ya ƙara da cewa, “A yanzu ya na da muhimmanci mu nanata cewa ita fa fatara da yunwa babu ruwan ta da batun wace jam’iyyar siyasa mutum ya ke bi.
“Saboda haka wannan Ma’aikata ta na taya mai girma Gwamnan Jihar Bauchi murna kan ƙaddamar da shirin sa na bayar da tallafi mai suna ‘Ƙaura Economic Empowerment Programme, KEEP) wanda ya ƙaddamar kwanan nan, sannan ta na yi masa marhabin da zuwa wajen taya ta gagarumin yaƙin da ta ke yi da fatara da yunwa a Nijeriya, musamman ma dai a Jihar Bauchi.”
Discussion about this post