A sanarwar haka wanda kwamishinan ilimin jihar ya sanar ranar Litinin ya ce za a kafa kwamiti nan bada dadewa domin duba sake tantance makarantun jihar duka da sabunta lasisin su.
Hakan na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin kawo karshen cin zarafi da ayyukan ta’addanci da wasu malamai suke yi wa yayan mutane dake karatu a makarantun su.
Idan ba a manta ba a cikin makaon jiya ne aka rufe wata makaranta da aka kama shugaban makarantan tare da wasu abokansa da iyalansa sun yi garkuwa da wata daliba mai shekaru 5 suka kashe ta bayan sun karbi kudin fansa daga iyayen dalibar.
Abin takaiaci shine bayan malamin ya dirka wa daliban guba ta mutu sai yayi gunduwagunduwa da naman jikin ta ya saka cikin buhu sannan ya binne ta a makaranta sa.
Ba a nan ya tsaya ba sai kuma ya koma ya ci gaba da zuwa gidan iyayen yarinyar yana taya su zaman tsammani da addu’o’i. idan ya koma gida kuma sai ya kira iyayaen yarinyar da ya riga ya kashe ta yayi musu barazanar zai kashe ta idan ba su cika masa sauran kudin fansar ba.
Daga karshe dai da dubun sa ta cika sai aka kama shi tare da sauran wadanda suka hada baki suka kashe wannan yarinya.
Discussion about this post