Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
‘Yan uwa na Zamfarawa! Wallahi ni har kullun ni kan yi mamaki kuma ni kan ji haushi da bakin ciki akan wasu lamurra da har yau akwai alamun cewa, ‘yan uwana talakawan jihar Zamfara sun kasa ganewa, kuma sun kasa fahimta. Misali, mutun ne zai shiga siyasa, shi ba kowa ba, kuma shi ba dan kowa ba. Shi ba dan kasuwa ba, kuma shi ba wani kasurgumin ma’aikacin gwamnati ba ko wani hamshakin dan kwangila ba. Ko da ya shiga siyasa, kowa yasan cewa baya da komai, wallahi ba shi da ko sisi, kawai yawo yake yi yana maula da banbadanci da roko a gidajen ‘yan siyasa. An san shi, an san iyayensa, an san asalinsa, an san tarihinsa, an san dukkanin zuri’arsu. Kowa ya shaida cewa shi dan talakawa ne iri na, amma kawai daga ya samu dama, bisa kaddarar Allah, da kuma sanadiyyar wasu mutane da suka daga shi sama, suka taimakeshi, suka tallafa masa, ya shiga siyasa, har Allah cikin ikon sa ya kaddari ya zama gwamnan jiha, yayi shekaru takwas yana matsayin gwamnan jiha, bayan wasu kananan mukaman siyasa da ya taba rike wa, sanadiyyar dai wadancan manyan mutane, bayin Allah, mutanen kwarai, wadanda basu da hassada da ganin kyashi; wadanda Allah yayi amfani da su suka tallafa masa, suka daga shi sama har ya zama wani abu a jihar. Kawai daga wannan, shi yanzu yana ganin ya zama biloniya, ya tara kudi, ta hanyar sace dukiyar jiha, ta hanyar kassara jihar, wanda har yake ganin yanzu, shi karfin shi ya kawo, wai shi zai iya ja da ikon Allah, wai zai iya ja da zabin Allah, zai iya ja da hukuma ko gwamnatin jiha!
Ya ku ‘yan uwa na talakawan jihar Zamfara, ku sani, wallahi a gaban idon mu aka kirkiro jihar Zamfara, duk gwamnonin da aka yi a jihar Zamfara a gaban idon mu suka yi mulki suka gama, suka wuce. Tun daga Jibril Bala Yakubu, har zuwa Yarima, har zuwa Dallatu, wallahi bamu gani ba, kuma bamu ji cewa sun saci kudin al’ummah ba, bamu ga sun sace dukiyar jiha ba, basu sace dukiyar talakawa ba, basu jefa al’ummah cikin wahala, da kangi da kunci ba, bare wai har suce zasu yi amfani da dukiyar da suka sata ta jiha, su rinka sayen tirelolin abinci da milliyoyin dabbobi suna rabawa magoya bayansu na siyasa. Kawai abun da muka shaida game da su shine, wadancan tsoffin gwamnoni da suka shude, suna taimakawa talakawa ne da magoya bayan su, gwargwadon iyawarsu, da dan abunda Allah ya hore masu, kasancewar duk mun shaida cewa basu yi sata ba, kuma basu zalunci talakawan su da al’ummarsu ba!
Amma da yake mu talakawan jihar Zamfara, har yanzu, wasu daga cikin mu sun kasa ganewa, mun kasa fahimta, wasun mu basu waye ba, daga kawai mutum yayi gwamna, ya sace maku dukiya, yazo kuma yana sawo kayan masarufi yana rabawa magoya bayan sa, shike nan sai muyi ta ganin cewa wai taimako yake yi, wai abun kirki yake yi.
Shin kun manta da cewa, watakila da bai sace wannan dukiyar taku ba, da an samu tsaro da taimakon Allah, da an samu ruwan sha masu tsafta, da an samu ingantaccen ilimi, da an samu ingantacciyar wutar lantarki, da an samu magani kyauta a asibitocin mu, da an samu ingantattun hanyoyi da sauran kayayyakin more rayuwa a jihar Zamfara!
Kawai mutum ya halaka ku, ya sace maku dukiya, ya kashe ku, amma don ya dan tsakuri wani abu daga cikin dukiyar ku da ya debe, yana rabawa magoya bayansa dan wani abu, yana bushasha iya son ran sa, wanda kowa yasan wallahi ba don Allah yake yi ba, kawai yana yi ne domin ya kara rikita jihar Zamfara, ya kara jawo muna matsalolin rashin tsaro, ya zuga talakawa domin su bijirewa gwamnati mai ci, ta Matawalle zabin Allah, wanda dama can muna sane da halin da jihar mu take ciki, na halin rashin tsaro, wanda nayi imani da Allah cewa, shi wancan azzalumin mutum, yana daga cikin wadanda basu so wannan matsala ta kare ta jihar Zamfara, sannan yana daga cikin wadanda suka haddasa muna wannan bala’i a jiha!
Saboda haka, wallahi ina kira da babbar murya, kuma tsakanina da Allah, cewa, talakawan jihar Zamfara muyi hankali, ya zama tilas mu shiga taitayinmu, mu goya wa gwamnatin Matawalle baya, muyi masa addu’o’i, mu rokar masa Allah ya bashi nasara, muyi masa fatan alkhairi, da rokon gamawa lafiya.
Sam, kar mu yarda wasu shedanu, mashaya jinin bayin Allah, ‘yan iska, wadanda basu nufin jihar mu da alkhairi, su zuga mu, su kai mu su baro, da sunan wai wata adawar siyasa ta shedanci. Wallahi mun fi kowa sanin halin da jihar mu take ciki, na matsalar rashin tsaro. Don haka duk wanda yazo muna da wani rikici, ko wata hayaniya, ko wani rudu, da sunan wai shi dan adawar siyasa ne, ko da sunan wa’azi, don Allah, don Allah, don Allah ina rokon ku, da mu kunyata shi, ko shi waye, kuma ko shi dan gidan waye. Domin duk tunanin da mutum yake yi, wallahi mu jihar mu tafi shi daraja da matsayi a wurin mu, domin bamu da wani wurin da yafi muna jihar Zamfara a duniya!
Wallahi in dai har da gaske muke yi, muna son ci gaban jihar Zamfara da zaman lafiyar ta; in dai har muna son a samu zaman lafiya, muna son Allah ya tausaya muna, ya kawo muna karshen matsalolin da suka dabaibaye jihar mu, to ya zama tilas mu hada karfi da karfe, mu hada hannu, mu goyi bayan gwamnatin Bello Matawalle, muyi masa addu’a da fatan alkhairi!
Wallahi, Allah ya sani, kuma shine shaida, ni ban san Bello Matawalle ba, kuma shi bai san ni ba, to amma ni ina kishin jiha ta ta Zamfara tsakanina da Allah, kuma matsalolin jihar suna damu na matuka. Domin Allah ya sani, kuma shi shaida ne akan haka, kullun, da su nike kwana, kuma da su nike tashi!
Kuma wallahi ku sani, duk abunda Sheikh Sa’idu Aliyu Maikwano ya fadi a wurin tafsirinsa game da gwamna Matawalle da gwamnatinsa gaskiya ne, kuma ya zama tilas, kuma wajibi, kuma dole dukkanin Zamfarawa su rungumi wannan bayani nasa mai albarka, kuma suyi na’am da shi yadda ya kamata. Idan ba haka ba kuwa, wallahi zamu yi dana-sani! Allah ya sawwake, amin.
Ya ku ‘yan uwa na Zamfarawa masu daraja, ku sani, wallahi ina yi maku wannan bayani ne tsakanina da Allah, kuma domin Allah. Don haka ya rage namu, idan mun ji to sai Allah ya taimake mu, amma idan mun bijire, muka yi kunnen uwar shegu da wannan bayani, to mune zamu sha wahala ba wasu ba. Ko kuma in ce mune muke shan wahala ba wasu ba! Ina rokon Allah ya sawwake, amin.
Sannan ya zama tilas muyi hattara, kuma mu kiyaye, domin mutum ko shi malamin addini ne, in dai har muka ga alamun cewa zai kawo muna rudani da hayaniya a jihar mu, to ya zama dole mu ce masa ba mu yarda ba, kuma mu kauracewa shedancinsa da wawancinsa. Domin ba zai yiwu ba, mutum da sunan malanta, ko da sunan wai wata adawar siyasa, ya kara jefa mu cikin rudani da hayaniya marasa amfani! Mu jihar mu wallahi tafi karfin wani maganar APC ko PDP a wurin mu. Mu zaman lafiya muke bukata a halin yanzu ba wani abu ba. Don haka ya zama tilas mu goyi bayan gwamnatin Matawalle, a kokarin ta, tare da taimakon Allah da iyawarsa, na neman mafita da samar da zaman lafiya jihar.
Ya ku ‘yan uwana Zamfarawa, wallahi a halin yanzu kasar mu Najeriya da jihar mu ta Zamfara, da sauran jihohi, addu’a suke bukata, ba wata hayaniya ta shirme ba, ko wata adawar siyasa marar amfani ga talakawa ba.
Ina addu’a da rokon Allah yasa mu gane, amin.
Wassalamu Alaikum
Nagode
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.