Gwamnan Benuwai, Emmanuel Ortom ya maida wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai martani wai zargin wai ya zargi gwamnan da yin amfani da rashin tsaro a jihar sa da ya kasa warwarewa sai dangana shi yake da wai gazawa ce daga bangaren gwamnatin tarayya.
Ortom ta hannun Kakakin sa ya shaida cewa wannan magana da suka karanta bai yi musu dadi ba domin bai kamata ace kamar El-Rufai bane dake da guntun kashi a bayan sa zai fita yana irin wannan magana.
” Na fi karfin El-Rufai ya yi min Izgilanci domin shine abin tausayi, wanda matsalolin da ya kirkiro da hannun sa suka dabaibayeshi ya kasa warware su, ya kyale mutanen kaduna na ta iyo cikin kogin wahala da ra shin zaman lafiya, amma ya na wage baki a inda ba huruminsa bane.
” El-Rufai mai ci da addini ne, domin kowa ya san yadda ya dauki gatari ya datse zaman lafiya dake tsakanin ‘Yan Kaduna aka samu rarrabuwar kai a jihar, kuma ya kasa magance matsaloli da barakar da ya kirkiro su da hannunsa a jihar.
” Kai bari in gaya muku karara ku saurareni, El-Rufai na daga ciki, wadanda suka kai Buhari suka baro a kasar nan. Ba shi da hurumin da wai ace yau El-Rufai ne zai zargi gwamna Ortom na rashin tabuka komai, shi me yayi a Kaduna in banda barusa da raba kan jama’a.
” Kwana-kwanan nan ya kori ma’aikata akalla dubu 4000 a jihar sa. Wannan mutum ne mai tausayi. Bashi da ita.”
A takardar martanin da Ortom ya fitar wanda Channels TV ta wallafa a shafin a na yanar gizo ta inda Ortom ke shiga bata nan yake fita ba.
Sai dai kuma wannan Korafi da Ortom ke yi bisa kalaman jawabi da El-Rufai yayi bai kai ga PREMIUM TIMES HAUSA ta ganshi, tukunna.
Ortom ya ce ruwa ne yake neman ya kare wa El-Rufai, Buhari ya fara nesa-nesa da shi, shine ya ke so ya burge fadar shugaban kasa ta hanyan haurar gwamna Ortom.
Discussion about this post